Kasar Sin za ta kebe kudin Sin yuan miliya dari 1 daga baitulmalin tsakiya nata don horar da manoman da ke zama a kauyuka dubu 10 a kasar a fuskar kimiyya da fasaha na aikin noma.
Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu wannan labari ne daga ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin a ran 2 ga wata.
An ba da karin haske cewa, ko wane kauyen da kasar Sin ta zaba zai sami kudin horo yuan dubu 10. Masana masu ilmin aikin noma za su shirya kos na horo a cikin wadannan kauyuka, inda za su horar da manoma, za su kuma ba da ayyukan hidima a fannin kimiyya da fasaha na noma.
Bayanan kididdiga sun nuna cewa, manoman kasar Sin ba su da isasshiyar kwarewar kimiyya da fasaha, wannan ya kawo illa ga bunkasuwar aikin kawo albarka na noma da karuwar kudin shiga ga manoma.(Tasallah)
|