|
A ran 1 ga watan Satumba wato yau, Mahmud Ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya nanata cewa, Iran ba za ta watsi da ikonta na yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ba. Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Iran ya bayyana ra'ayinsa bayan karshen lokacin da aka kayyade cikin kuduri mai lamba 1696 da kwamitin sulhu na M.D.D. ya tsayar kan matsalar nukiliya ta Iran.
A wannan rana Mr. Ahmadinejad ya ce, wasu kasashe sun yi kokarin hana kasar Iran samun fasahar yin amfani da makamashin nukiliya cikin zaman lafiya bisa dalilan karya daban-daban, amma mutanen Iran ba za su yi watsi da irin wannan ikon da ba za a iya haramta musu ba ko kusa.
A wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ya bayyana cewa, Rasha ta yi nadama sabo da Iran ba ta dakatar da shirin tace sinadarin Urainum bisa bukatun da kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi mata ba. Nan gaba kadan kwamitin sulhu da sauran kasashe 6 wato Rasha da Amurka da kasar Sin da Ingila da Faransa da Jamus za su tattauna matsalar yadda za su dauki matakai kan kasar Iran. (Umaru)
|