Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-01 16:34:51    
Dandalin tattaunawa kan wasannin Olympics tsakanin kasa da kasa ya ba da shawarwari ga birnin Beijing a fannin bunkasa al'adu da raya birnin

cri

Sana'ar kirkiro fasalin al'adu, wata sana'a ce da ta fi jawo hankulan kasashen kasa da kasa a halin yanzu. Ta yaya za a iya hada taron wasannin Olympics da sana'ar kirkiro fasalin al'adu da kyau? Lallai wannan wani muhimmin batu ne da ake sha'awar tattauna a kai. A gun ' Dandalin tattaunawa kan aikin kirkiro fasahlin al'adun wasannin Olympics da raya birnin dake daukar nauyin bakuncin taron wasannin Olympics', wanda aka kammala shi kwanan baya ba da dadewa ba, dimbin kwararru da masana sun fadi albarkacin bakinsu kan taron wasannin motsa jiki na Beijing a shekarar 2008 da kuma yadda za a bunkasa sana'ar al'adu ta Beijing.

Wannan dandalin tattaunawa, wani muhimmin abu ne dake cikin bikin al'adu na 4 na wasannin Olympics na shekarar 2008, wanda yanzu ake gudanar da shi. Shahararrun kwararru da masana fiye da 10 na kasashen Burtaniya, da Amurka ,da Holland, da Canada da Australiya da kuma na kasar Sin halarci dandalin tattaunawar.

Mr. John Howkins, mashahurin masanin tattalin arziki na kasar Burtaniya ya zo nan Beijing musamman don halartar dandalin tattaunawar, inda ya yi hasashen, cewa hanyoyin da akan bi wajen samun nasara ko a fannin wasannin motsa jiki ko a fannin fasaha sun tashi daya. Ya shawarci gwamnatin birnin Beijing da ta yi amfani da kyakkyawar damar shirya taron wasannin Olympics a shekarar 2008 domin tattara 'yan wasa mafi kwazo da kuma nagartattun 'yan fasaha na duniya gu daya. Mr. Howkins ya furta, cewa: ' A ganina, taron wasannin Olympics, ya kasance tamkar zarafi ne ga birnin Beijing na gwada kyakkyawar fuskarsa ga jama'ar duk duniya, wadanda za su gano cewa dukkan mazauna birnin suna iya bayyana ra'ayoyinsu ko a fannin fasaha ko a fannin al'adu'.

Yanzu, kafofin watsa labaru da ra'ayoyin bainal jama'a na kasar Sin duk sun dauka, cewa kamata ya yi birnin Beijing har duk kasar Sin baki daya su kama wannan kyakkyawar damar shirya taron wasannin Olympics domin raya birnin da kuma bunkasa tsarin sana'o'i na birnin. Amma, duk da haka, wani shahararen masani mai suna Xu Zhuoquan na kasar Sin wanda ke halartar dandalin tattaunawar ya bayyana ra'ayinsa daban. Mr. Xu Zhuoquan, shi ne babban mai sa ido kan cibiyar nazarin manufofin al'adu ta Hongkong kuma wani mashahurin masanin ilmin gini ne. Ya furta, cewa : 'Lallai taron wasannin Olympics wata kyakkyawar dama ce domin ma iya bunkasa abubuwa da dama daga wajensa. Amma ko da babu taron wasannin Olympics, mu kam ya kamata mu ma mu bunkasa wadancan abubuwa domin suna da muhimmancin gaske ga raya birnin Beijing. Aikin raya birnin, wani makasudi ne namu ; Amma taron wasannin Olympics, wani taron wasannin motsa jiki ne wanda akan kashe rabin wata kawai ana gudanar da shi. Don haka, tilas ne mu yi la'akari da yadda za a hada aikin raya birni da taron wasannin Olympics kamar yadda ya kamata'.

Mr. Jin Yuanpu, shehu malami daga Jami'ar jama'ar kasar Sin ya fi mai da hankali kan aiki raya birni bayan taron wasannin Olympics. Mr. Jin Yuanpu, shi ne darakan cibiyar nazarin taron wasannin Olympics na zamantakewar al'adu, wadda aka kafa a shekarar 2000. Ya fadi, cewa tattalin arziki na wasannin Olympics, wani kashi ne mafi muhimmanci dake cikin hasashen wasannin Olympics da kuma al'adun wasannin Olympics. Wata hanyar da muka gano, ita ce bunkasa sana'ar kirkiro daga dukkan fannoni.

Ko shakka babu bambancin ra'ayoyin da aka gabatar sun samar da wata sabuwar hanyar yin tunani ga kwamitin shirya taron wasannin Olympics na Beijing da kuma masu tsarin fasalin bunkasa birnin. Shugaban kwamitin Mr. Jiang Xiaoyu ya yi hasashen, cewa : 'Bikin al'adun Olympics da aka soma yinsa a shekarar 2003, ba ma kawai ya yada ilmin wasannin Olympics ga jama'a ba, har ma ya tattara karfin da kwararru da kuma masana suke da shi na nuna goyon baya ga taron wasannin Olympics na shekarar 2008.'.

Mr. Jiang Xiaoyu ya kara da, cewa hasashen shirya taron wasannin Olympics da gwamnatin birnin Beijing ta fito da shi, shi ne : ' Wasannin Olympics na kore-shar, da wasannin Olympics na kimiyya da fasaha da kuma wasannin Olympics na zamantakewar al'adu', wato 'Green Olympics, High-Tech Olympics and Peaple's Olympics' a Turance .( Sani Wang )