Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-09-01 14:48:52    
Kwamitin Sulhu na M.D.D. ya tsaida kuduri cewa, sojojin M.D.D. za su ci gajiyar nauyin kiyaye zaman lafiya na shiyyar Darfur

cri

Ran 31 ga watan Agusta, kwamitin sulhu na M.D.D. ya zartas da kuduri mai lamba 1706, inda ya tsaida kudurin aikawa da sojojin M.D.D. zuwa yankin Darfur ta kasar Sudan, bayan da sojojin kungiyar tarrayar kasashen Afrika suke gama wa'adin aikinsu a karshen watan Satumba na shekarar da muke ciki, domin ci gajiyar nauyin kiyaye zaman lafiya, haka kuma za su iya ba da taimako ga gwamnatin sudan da dakarun da ke yin adawa da gwamnati da su tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya ta
Darfur da suka cimmawa a watan Mayu na shekarar da muke ciki.

Bisa kudurin, za a habaka yawan masu aikin soja na kungiyar musamman na M.D.D. da ke kasar Sudan daga dubu 10 na yanzu zuwa dubu 17.3, kuma za a kara aika da rukunin 'yan sanda da yawansu ya kai 3300. Bayan haka kuma, kudurin ya ba da cikakken iko ga sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D., wato su iya daukar duk matakan da suka wajabta, domin kiyaye kwanciyar hankali na 'yan M.D.D. da gine-ginensu, da kare farar hula daga barazanar hare hare, da kuma tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.



A sa'i daya kuma, kudurin ya kayadde cewa, ba za a iya girke sojojin kiyaye zaman lafiya a shiyyar Darfur ba, face sai gwamnatin kasar Sudan ta yarda da wannan.

Kasashen Sin da Rasha da Katar sun kaurace wa jefa kuri'u kan kudurin. Mr. Wang Guangya, wakilin dindindin na kasar Sin da ke M.D.D. ya yi bayani bayan da aka jefa kuri'u cewa, kullum kasar Sin tana nuna ra'ayi mai yakini a lokacin da take hallartar tattaunawar da ke da nasaba wajen warwar rikicin Darfur, kuma tana goyon bayan yawancin abubuwan da ke cikin wannan kuduri. Amma, tana tsayawa kan matsayinta wajen lokacin da aka zartas da kuduri, da kuma wasu abubuwan da aka rubuta a cikin kuduri, sabo da haka ta kaurace wa jefa kuri'a.

Mr. Wang Guangya ya nuna cewa, warware hargitsin Darfur aikin gaggawa ne da mai rikitawa, ya kamata ana da karfin zuciya, da manufofi masu amfani, da kuma yin hakuri kan matsalar nan. Yanzu, lokacin jefa kuri'a a kan kuduri bai yi ba sabo da gwamnatin Sudan tana tsayawa kan kin yarda da wannan, ya kamata M.D.D. ta tattauna sosai da gwamnatin Sudan. Wang Guangya ya ce, sojojin M.D.D. su gaji nauyi wannan wani zabi mai hakika ne, amma a sa'i daya tilas ne gwamnatin kasar Sudan ta yarda da wannan kafin a aiwatar da ayyuka. Wannan shi ne kuduri daya na kungiyar tarrayar kasashen Afrika, shi ne kuma ra'ayi daya na kwamitin sulhu.



Nana Effah-Apenteng, shugaban kwamitin sulhu na wannan wata, kuma wakilin dindindin na kasar Gana da ke M.D.D. ya bayyana cewa, M.D.D. za ta ci gaba da yin cudanya da gwamnatin Sudan, kuma za ta yi tattaunawa a tsakanin manyan shugabanni a lokacin da za a shirya sabon babban taron M.D.D.. Bayan haka kuma ya ce, zartas da wannan kuduri ba ya nuna cewa, an riga an rufe kofar ci gaba da yin tattaunawa da shawarwari da gwamnatin Sudan. Mr. Effah-Apenteng ya yi kira ga kungiyoyin kasashen duniya masu karfi kan hargitsin Darfur, kamar su kungiyar tarrayar kasashen Afrika, da kungiyar tarrayar kasashen Larabawa, da kuma kungiyar taron musulmi, da dai sauransu, da su halarcin tattaunawar. Bisa labarin da muka samu an ce, a 'yan kwanaki masu zuwa, M.D.D. za ta kira taron da ke da nasaba, domin ci gaba da tattauna hargitsin Darfur, da kuma hanyoyin warware hargitsin. (Bilkisu)