Ran 31 ga watan jiya, wani jami'in ma'aikatar cikin harkokin gida ta kasar Iraki ya bayyana cewa, a wannan rana, an sha tayar da hare-haren boma-bomai a wuraren gabashin birnin Bagadaza, sakamakon haka mutane 43 suka riga mu gidan gaskiya, wasu 126 sun jikkata.
Wata majiya daga ma'aikatar cikin harkokin gida ta kasar ta ce, da misalin karfe 7 na daren wannan rana, an tayar da hare-haren boma-bomai har sau uku a wurare da ke gabashin birnin Bagadaza, inda mutane da yawa suka mutu ko ji raunuka. Daya daga cikin hare-haren an tayar da shi ne a unguwar Al-Ameen, sauran biyu kuwa sun auku ne a unguwar Al-Baladeat.
A wannan rana da safe, an kai harin kunar bakin wake na fashewar boma-bomai da aka dasa a cikin mota a wani gidan mai da ke a gabashin birnin Bagadaza, inda mutane hudu suka bakunci lahira, wasu 11 sun jikkata. (Halilu)
|