A ran 31 ga wata, Mahmoud ahmadinejad, shugaban kasar Iran ya bayyana cewa, Iran ba za ta durkusa a gaban matsin da kasashen yamma suke yi mata ba ko kusa, kuma ko kusa ba za ta yarda kowane mutun ya take ikon kasar Iran ba.
Yayin da Mr. Ahmadinejad yake yin jawabi a wannan rana a birnin Orumiyeh da ke arewa maso yammacin kasar Iran ya ce, ya kamata kasashen Yamma su gane cewa, Iran ba za ta mika wuya ga irin matsin da ake yi mata ba, kuma ko kusa ba za ta yarda da kowane mutun ya take ikon kasar Iran ba. Shugabannin kasar Amurka suna ganin cewa za su iya daidaita dukkan matsaloli ta hanyar nuna karfin makamai, amma wancan zamani ya riga ya wuce. Ya ce, jama'ar Iran suna hada kansu gu daya.
A wannan rana, Frand-Walter Steinmeier, ministan harkokin waje na kasar Jamus ya yi kashedi cewa, idan kasar Iran ba ta aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na M.D.D. ya zartar kan matsalar nukiliya ta Iran ba, za a kayyade karfinta wajen tafiyar da harkokin kasashen duniya. (Umaru)
|