Ran 30 ga wata, kwamitin koli na tsaro na kasar Portugal ya tsai da kudurin cewa, za ta aika da sojoji 140 zuwa kasar Lebanon don shiga sojojin wucin gadi na MDD da ke kasar.
Janar Demelo kakakin kwamitin koli na tsaro na kasar Portugal ne ya ba da wannan labari cewa, Anibal Cavaco Silva shugaban kasar Portugal da Jose Socrates firaministan kasar sun halarci taron da kwamitin ya yi a wannan rana. Bisa bukatar da MDD da kungiyar gammayar kasashen Turai suka yi, an tsai da kudurin aika wa da runduna mai sojoji 140 zuwa kasar Lebanon don shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya da MDD ke tafiyarwa.
|