Mun sami labari cewa, yawan karfin lantarki da kasar Sin ta bayar a shekarar da ta wuce ya kai kusan kilowatts-awa biliyan 2500, wato ya karu da fiye da kashi 13 cikin 100 bisa na makamancin lokaci na bariya.
Mun sami labari daga wani taron manema labaru da aka yi a ran 31 ga wata cewa, yawan karfin lantarki da kasar Sin ta bayar a shekarar da ta wuce ya karu da sauri, kuma karfin samar da wutar lantarki ya karu-karuwar gaske, wato a da yawan wutar lantarka da aka samar bai ishi mutane ba amma yanzu an daidaita wannan sabani sosai. Amma a sa'i daya mutane na wannan sana'ar sun bayyana cewa, har ila yau ya kasance da wasu matsaloli cikin masana'antar ba da karfin lantarki ta kasar Sin, kamar tsarin samar da wutar lantarki bai dace yadda ya kamata ba, kuma makamashin da ake amfani da su domin aikin kawo albarka sun yi yawan gaske.
Bisa shirin da aka tsara an ce, nan gaba kasar Sin za ta rubanya kokari domin kyautata tsarin ba da karfin lantarki, da kara saurin bunkasa masana'antar ba da karfin lantarki mai inganci. (Umaru)
|