Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-31 17:25:51    
Kasar Sin ta kammla nazarin yin amfani da allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye a asibiti bisa mataki na farko

cri

An bayar da wani labari mai faranta rai, cewa kwanakin baya ba da dadewa ba, kamfanin harhada magunguna na Ke Xing na kasar Sin da cibiyar riga-kafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin sun hada gwiwa wajen nazarin yin amfani da allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye a asibiti a mataki na farko. Sakamakon nazarin ya tabbatar da, cewa irin wannan allura ba ta yin illa ga jikin mutane. Yanzu, sashen da abun ya shafa ya himmantu wajen share fage ga aikin gabatar da rokon yin nazarin irin wannan allura a asibiti bisa mataki na biyu.

An bayyana cewa, akwai mutane masu aikin sa kai 120 da suka shiga cikin gwajin yin amfani da irin wannan allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye a asibiti bisa mataki na farko. Mr. Yin Weidong, manajan kamfanin harhada magunguna na Ke Xing kuma jami'in kula da harkokin nazarin yin amfani da irin wannan allura da aka yi a wannan gami ya bayyana, cewa : ' Mun yi allurai iri daban daban na riga-kafin cutar murar tsuntsaye a jikunan mutane 120, wadanda ba su mayar da martani mara kyau ba bayan da aka yi gwajin kan jikunansu .'

Jama'a masu sauraro, idan ba a manta ba, mutane da yawa sun kamu da kwayoyin cutar murar tsuntsaye a kasashen Vietnam, da kuma Thailand da dai sauransu tun bayan shekarar 2003. Sakamakon haka, kwararru da dama a fannin likitanci sun nuna damuwa kan yiwuwar yaduwar irin wadannan miyagun kwayoyi a fadin duk duniya. Bisa wannan yanayi dai, kasashen Sin da kuma Amurka da dai sauransu sun soma yin nazarin yin amfani da allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye a asibiti bisa taimakon kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO.

Allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye da kasar Sin ta yi nazari a kai a asibiti sun hada da allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye da kuma allurar riga-kafin kwayoyin cutar murar tsuntsaye da dai sauran ire-iren allurai. Kafin wannan, kasashen Amurka, da Fransa da kuma Australiya sun rigaya sun sanar da sakamakon gwaje-gwajen da suka yi a asibiti wajen yin amfani da allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye ; amma dukkan allurai da aka yi na riga-kafin kwayoyin cutar murar tsuntsaye ne, wato Split-Virus Vaccine a Turance ; Ita kasar Sin kuwa ta yi nazarin harhada irin wannan magani ne na riga-kafin cutar murar tsuntsaye wato Whole Virion Inactivated Vaccine a Turance.

Ban da wannan kuma, kasar Sin ta yi nazarin harhada irin wannan magani ne ta hanyar canza kwayoyin halitta wato Reverse Genetics. Hakan ya bada tabbaci ga ingancin allurar riga-kafin cutar murar tsuntsaye da akan yi amfani da ita domin mutane.

Mr. Yin Weidong ya kuma kara da ,cewa irin wannan allura da kasar Sin ta yi nasarar kirkiro shi, allura ce ta hudu da aka samu a duniya sakamakon gwaje-gwajen da aka yi a asibiti. Lallai kasar Sin ta tsaya daram a gaban zamani wajen nazarin irin wannan allura dake da amfani mafi muhimmanci ga lafiyar jikin jama'a na duk duniya. Ya kuma furta, cewa ' Yawancin ayyukan nazarin harhada magungunan riga-kafin cutar murar tsuntsaye, ana yinsu ne a manyan masana'antun kasashe daban daban masu sukuni, wadanda yanzu suke kan matsayin yin gwaje-gwaje a asibiti.'

Mun samu labarin, cewa domin ba da tabbaci ga yin aikin nazari lami-lafiya, kamfanin harhada magunguna na Ke Xing ya kuma gyara ma'aikatar harhada magungunan riga-kafin ciwon mura na yanayi-yanayi don ta harhada magungunan riga-kafin cutar murar tsunsaye, ta yadda za a iya tunkarar batun aukuwar annobar cutar mura. Ana sa ran kammala aikin gyaranta daga dukkan fannoni a shekarar 2007. ( Sani Wang )