Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-31 16:29:50    
Shugaban Iran ya yi kira ga kasashen Turai kada su garkama wa kasarsa takunkumi

cri

Ran 30 ga wata, shugaban kasar Iran Mr. Mahmud Ahmadinejad ya yi kira ga kasashen Turai da kada su garkama wa kasarsa takunkumi bayan ran 31 ga watan Agusta, ya kuma bayyana cewa, matakan horo da kwamitin sulhu zai dauka ba za su tilasta wa kasar Iran yin watsi da shirin nukiliya ba.

Lokacin da yake yin shawarwari da tsohon firaministan kasar Spain Mr. Felipe Gonzalez da ke ziyarar kasar Iran a ran nan, Mr. Ahmadinejad ya bayyana cewa, garkama takunkumi ba zai karya kwarin gwiwar mutanen kasar Iran ba. Ya yi fatan cewa, kada kasashen Turai su bi kasar Amurka, kada su yi sanyawa kasar Iran takunkumi, a maimakon haka, ya kamata su tsai da kudurin da abin ya shafa da kansu, kuma su warware matsalolin da ake fuskanta a yanzu ta hanyar yin shawarwari.(Tasallah)