Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-31 16:28:13    
Mahukuntan birnin Shanghai za su je kasar Amurka da Canada don daukar kwararru masu dalibta

cri
Jaridar People's Daily ta ba da labari a ran 31 ga watan Agusta cewa, don samun kwararru masu yawa da ke kasashen waje, wadanda za su sa kaimi kan ayyukan gina birnin Shanghai da ya zama birni na kasa da kasa na zamani da kuma cibiyar kasa da kasa a fannonin tattalin arziki da kudi da ciniki da sufuri kan teku, hukumar kula da ma'aikata ta birnin Shanghai za ta ja goranci hukumomi 27 na birnin da su je biranen San Francisco da New York na kasar Amurka da birnin Toronto na kasar Canada don daukar kwararru na gurabun aiki fiye da 2000 a ran 9 da 16 da 17 ga watan Satumba.

Kwararru masu dalibta da ke kasashen waje da za a nema a wannan gami sun nuna kwarewarsu a fannonin nazarin kimiyyar harkar ilmi da fasahar labaru da magungunan halittu da ilmin injiniya na software da aikin inshora da kudi da kula da dukiyoyi da zane-zanen gine-gine da dai sauransu.(Tasallah)