Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-31 12:20:22    
Dumamar yanayi ta kawo illa ga kasashe masu tasowa, in ji Bankin Duniya

cri
A cikin rahoto mai dumi-dumi da ya bayar a gun babban taron kasashe mambobin Asusun muhalli na kasa da kasa na karo na 3, Bankin Duniya ya nuna cewa, dumamar yanayi ta kawo wa muhallin duniya da bunkasuwar dan Adam illa, musamman ma a kasashen Afirka da wasu kasashen da ke kan tsibirai.

Rahoton ya yi bayanin cewa, saboda farin da sauye-sauyen yanayi ke kawowa, daga cikin ayyukan noma da ke kudancin Sahara wadanda Bankin Duniya yake ba su taimako domin yaki da talauci, kashi daya bisa hudu ne ke fuskantar matsaloli. A sakamakon karuwar leburin teku da bala'i daga indallahi, ya kan lalata gine-ginen samar da ruwa da sauran muhimman gine-gine a wasu kananan kasashen da ke kan tsibirai. Bincike da dama da aka yi sun tabbatar da cewa, sauye-sauyen yanayi zai kawo wa kasashe masu tasowa babbar illa a fannin tattalin arziki.(Tasallah)