Gwamnatin kasar Sin ta nuna kulawa sosai ga bala'in ambaliyar ruwa da kasar Koriya ta arewa ke fama da shi, kuma ta riga ta yanke shawarar bai wa Koriya ta arewa taimakon jin kai da suka hada da abinci da man diesel da magunguna da dai sauransu.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Qin Gang ya bayar da wannan labari ne a yayin da yake amsa tambayoyin da abin ya shafa a yau ran 30 ga wata a nan birnin Beijing.
A karshen watan da ya gabata, an sami aukuwar ambaliyar ruwa a kasar Koriya ta arewa, bisa rahoton da kungiyar kula da abinci da aikin noma ta MDD ta bayar, an ce, sakamakon bala'in, mutanen Koriya ta arewa dubu 60 sun rasa gidajensu, kuma gonakin da fadinsu ya kai kadada dubu 30 sun lalace, hasarar hatsin da aka yi ta kai kimanin ton dubu 100.(Lubabatu)
|