A ran 30 ga wata, kwamitin kungiyar Tarayyar Turai ya sanar da cewa, kungiyar Tarayyar Turai, wato EU za ta samar wa kasar Lebanon taimakon kudin da zai kai kudin Euro miliyan 42 domin sake gina kasar. Sakamakon haka, ya zuwa yanzu, bayan kawo karshen wutar yaki a tsakanin Isra'ila da Lebanon, jimlar kudin taimakon da kungiyar Tarayyar Turai ta samar wa Lebanon ta riga ta kai fiye da kudin Euro miliyan dari 1.
Benita Ferrrero-Waldner, wakiliyar kungiyar Tarayyar Turai wadda ke kula da aikin tsara manufofin diplomasiyya da na neman jituwa a tsakanin kasashen da suke makwabtaka da juna ta bayyana cewa, muhimmiyar nasarar da za a ci wajen sake raya kasar Lebanon ita ce gwamnatin Lebanon ta zama wata gwamnatin da take da cikakken ikon mulkin kasar cikin 'yanci. Sa'an nan kuma, dole ne a aiwatar da yarjejeniya mai lamba 1701 ta kwamitin sulhu na M.D.D. yadda ya kamata. (Sanusi Chen)
|