Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 21:19:56    
Gabas ta tsakiya, aljannan da ta kama gobara

cri

Tambayar da za mu amsa a yau ta fito ne daga hannun malam Iliyasu Bawa Karshi, mazaunin birnin Abuja na tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, ina son a ba ni tarihin kungiyar 'yan Hezbollah wanda ke kasar Lebanon, da makasudin yake-yaken da ake yi a yankin gabas ta tsakiya. A cikin dogon lokaci, gabas ta tsakiya inda ake shan samun wutar yake-yake ya dauki hankulan gamayyar kasa da kasa kwarai da gaske. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu tattauna wannan batu tare.

Kungiyar Hezbollah kungiyar siyasa da ta soja ce ta 'yan Shi'a na kasar Lebanon. Kungiyar ta fito ne a shekara ta 1982, wato lokacin da aka shiga shekara ta 7 ta yin yakin basasa a Lebanon. A lokacin, Isra'ila ita ma ta kai hare-hare kan Lebanon, har ma sakamakon hare-haren, musulmi 'yan Shi'a kusan dubu 600 sun kwarara zuwa kudancin birnin Beirut, babban birnin Lebanon. Wadannan 'yan gudun hijira dai ba su da gidajen kwana da kuma aikin yi, kuma suna matukar son samun wata kungiyarsu, su koma gida. Sabo da haka, bisa goyon bayan da Iran ta nuna musu, kungiyar Hezbollah ta fito, kuma sannu a hankali ta bunkasa har ta zama wata kungiyar dakaru da ke da 'yan sari-ka-noka sama da 5000.

Bayan da aka kawo karshen yakin basasa na Lebanon a shekara ta 1990, rukunoni daban daban na Lebanon sun kwance damararsu bisa kudurin gwamnatin kasar, amma ita kungiyar Hezbollah ba ta kwance damararta ba, sabo da a cewarta tana yaki da Isra'ila.

A kan maganar shawarwarin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya, kungiyar Hezbollah ta tsaya haikan a kan kin yin shawarwarin shimfida zaman lafiya, kuma a ganinta hanya daya tak da za a iya bi wajen warware matsalar da ke tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila ita ce murkushe Isra'ila. Manufar kungiyar Hezbollah ita ce maido da yankunan da Isra'ila ta mamaye ta hanyar nuna karfin tuwo.

Sabo da haka, har kullum Isra'ila ta dauki kungiyar Hezbollah a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, kuma ta mai da hankalinta a kan kai hare-hare ga wannan kungiyar.

Rikicin da ke tsakanin Lebanon da Isra'ila a watan Yuli da watan Agusta na shekarar da muke ciki ya barke ne ba zato ba tsammani, amma hasali ma dai, aukuwarsa ya zama dole. A yayin da sojojin Isra'ila ke kokarin daukar matakan soja a zirin Gaza, dakarun kungiyar Hezbollah ta bude wani 'sabon fagen yaki' a kan iyakar da ke tsakanin Lebanon da Isra'ila, nufinta shi ne ba da tallafi ga kungiyar Hamas da ke yaki da Isra'ila da sassauta wahalolin da Palasdinawa suke sha sakamakon hare-haren sojojin Isra'ila, haka kuma don jefa Isra'ila cikin mawuyacin hali na yaki da bangarori biyu.

A sa'i daya kuma, a matsayinta na kungiya daya tak da aka amince da ke da ikon mallakar dakaru bayan yakin basasa na Lebanon, kungiyar Hezbollah tana fuskantar hadarin rasa makaman da ke hannunta. Shi ya sa kungiyar Hezbollah tana matukar bukatar bangarori daban daban na kasar da su sami ra'ayin cewa, Isra'ila tana ci gaba da zama barazana mafi tsanani da ke gaban Lebanon, kuma kasancewar dakarun yaki ta ci gaba da zama dole.

Daga nata bangaren kuma, wani muhimmin dalilin wannan yakin da Isra'ila ta gabatar a kan kungiyar Hezbollah ta Lebanon shi ne, har kullum, Isra'ila tana daukar kungiyar Hezbollah a matsayin kayar da ta tsone mata ido, a waje daya kuma, da kyar a tabbatar da kudurin MDD na kwance damarar kungiyar Hezbollah, sabo da haka, Isra'ila tana son yin amfani da wannan dama, ta cire kungiyar Hezbollah daga yankunan kan iyaka.

Gabas ta tsakiya ta kasance daya ne daga cikin kyawawan yankuna masu arziki da albarka na duniya. Amma wannan aljannan duniya tana daukar rikice-rikicen da suka fi karfinta. A nan wurin, al'ummar Yahudawa da al'ummar Larabawa sun yi ta ci gaba da rikicin da ke tsakaninsu yau da gobe, tare kuma da tsoma baki daga rukunonin waje, duk sun sa wannan karamin yanki ya zamo mahadar rikice-rikice iri iri. A cikin shekaru 60 bayan yakin duniya na biyu, yawan manyan yake-yaken da aka samu a wannan yanki ya kai kusan goma, kuma daga cikinsu, biyar sun auku ne a tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila, balle ma kananan rikice-rikice marasa lisftuwa.

Amma kuma, yake-yaken da aka samu a gabas ta tsakiya sun kuma nuna mana cewa, yaki bai taba zama dabara mai kyau a wajen warware matsaloli ba. Don tabbatar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, ana bukatar bangarori daban daban da su yi shawarwari cikin daidaici, kuma su nemi ra'ayi daya a yayin da suke yarda da kasancewar bambancin ra'ayi, su samu bunkasuwa tare, ta yadda za a kashe wutar yaki da ke wannan wuri.(Lubabatu)