Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 18:28:37    
Kasar Sin ta kaddamar da dokar shigi da ficin namun daji da tsire-tsiren daji

cri
Tun daga ran 1 ga watan Satumba, "Dokar sa ido kan shigi da fici namun daji da tsire-tsiren daji da suke fuskantar barazanar gushewa daga duniya", za ta fara aiki. Wannan dokar farko ce mai muhimmanci da gwamnatin kasar Sin ta tsara domin sa ido kan ayyukan shigi da ficin namun daji da tsire-tsiren daji da suke fuskantar barazanar gushewa daga duniya.

Bisa wannan doka, za a hana cinikin namun daji da tsire-tsiren daji da suke fuskantar barazanar gushewa a tsakanin kasa da kasa. Amma idan ana son shigi ko ficin irin wadannan namun daji da tsire-tsiren daji domin yin nazarin kimiyya ko kiwonsu, dole ne a samu amincewa daga hukumomin kasar Sin da ke kula da harkokin namun daji da tsire-tsiren daji. (Sanusi Chen)