A ran 29 ga wata da yamma, yayin da Sergey Lavrov, ministan harkokin waje na kasar Rasha ke ba da amsa ga tambayoyin da hadaddiyar kungiyar ba da bayanai ta "ziyarar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha" ta yi masa, ya jinjina sosai ga wannan ziyarar da ake yi, ya bayyana cewa, ziyarar nan ta ba da babban taimako ga kara dankon zumunci tsakanin kasashen 2 wato Sin da Rasha. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilanmu suka ruwaito mana wanda yake da lakabin haka, "Ministan harkokin waje na Rasha ya jinjina sosai ga ziyarar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha".
Mr. Lavrov da farko ya jinjina sosai ga ziyarar sada "zumunci tsakanin Sin da Rasha", ya bayyana cewa, "zumunci tsakanin Sin da Rasha" ta ba da taimako ga kara fahimtar da jama'ar Sin kan kasar Rasha ta yanzu, kuma ta ba da babban taimako ga kara dankon zumunci tsakanin kasashen 2 wato Sin da Rasha. Yana fatan bayanan da 'yan jaridun kasar Sin suka bayar za su iya kara taimaka wa jama'ar Sin wajen fahimtar kasar Rasha yadda ya kamata kuma daga duk fannoni. Mr. Lavrov ya kuma jaddada cewa, ya kamata a nuna godiya ga Rediyon kasar Sin wanda ya tsara shiri da daukar nauyin wannan babban aiki. Ya ce, "Ziyarar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha" wani aiki ne da ba a taba yin sa ba a tarihi. Manema labaru fiye da 40 na kasar Sin sun kai ziyara a birane 18 na Rasha cikin kwanaki fiye da 40 kawai, ina tsammani cewa, har da Rashawa da yawa su ma suna sha'awar ziyarar da kuke yi. Muna nuna godiya ga 'yan kungiyar "Ziyarar sada zumunci tsakanin Sin da Rasha", musamman ma ga hukumar da ta ba da shawara da daukar nauyin wannan aiki wato Rediyon kasar Sin, domin ku ne kuke daukar muhimman ayyuka ga yin wannan ziyarar."
Yayin da Mr. Lavrov ya tabo magana kan dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 ya bayyana cewa, babu kowane irin sabani a tsakanin Sin da Rasha wajen siyasa, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen 2 ya riga ya shafi fannoni daban-daban na dangantakar. Ya ce, dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha tana cikin lokaci mafi kyau na tarihi, dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 wajen muhimman tsare-tsare tana da makoma mai haske. Ya amince cewa, irin wannan dangantaka a tsakanin Sin da Rasha ta zama muhimmin abun ne ga shimfida zama mai dorewa na duniya. Ya ce, "Bunkasuwar da ake samu wajen dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha tana da saurin gaske. Ban da hadin gwiwar da ake yi tsakanin bangarorin 2, kuma muna yin shawarwari da hadin gwiwa kan dandalin kasa da kasa. Dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha ba ta da ta 2 a duniya wajen fannoni da yawa, mu ne manya kasashe 2 da ke makwabtaka da juna. Rasha da Sin kasashe 2 ne wadanda dukkansu suna da dogon tarihi da al'adu mai haske, dukkan su suna girmama wa juna, kuma sun daidaita dukkan matsalolinsu ta hanyar yin shawarwari da zaman lafiya."
Sa'an nan kuma Mr. Lavrov ya bayyana cewa, Rasha tana nan tana kokarin share fage domin "Shekarar kasar Sin ta Rasha" wato shekara mai zuwa, ya ce, "Yanzu muna nan muna kokarin share fage domin "Shekarar kasar Sin ta Rasha" wato shekara mai zuwa, za mu iya tsamo fasahohin da kasar Sin ta samu wajen yin bukukuwan "Shekarar Rasha a kasar Sin" a wannan shekara."
|