Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-30 10:53:14    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(24/08-30/08)

cri
Ran 28 ga wata, a nan Beijing, a hukunce ne aka fara daukar masu aikin sa kai domin gasannin taron wasannin Olympic da na nakasassu da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008 mai zuwa.

An ba da karin haske cewa, za a bukaci masu aikin sa kai kimanin dubu 70 domin gasannin taron wasannin Olympic na Beijing, wasu dubu 30 domin gasannin taron wasannin Olympic na nakasassu, za a fi daukar masu aikin sa kai a nan Beijing, musamman ma a jami'o'i da kwalejoji na Beijing. A sa'i daya kuma, za a daukar wasu masu aikin sa kai daga dukan mutanen kasar Sin da 'yan uwanmu na Hong Kong da Macao da Taiwan da Sinawa 'yan kaka gida da kuma dalibai masu dalibta da kuma mutanen kasashen waje. Mutanen da suka nemi zama masu aikin sa kai sun fara yin rajista tun daga ran 28 ga watan Agusta har zuwa karshen watan Maris na shekarar 2008.

Ran 27 ga wata, 'yan wasan kasar Sin Zheng Jie da Yan Zi sun lashe 'yan wasan kasashen Amurka da Australia da cin 2 ba ko daya, ta haka sun zama zakara a cikin gasa ta tsakanin mata biyu biyu ta budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta New Haven ta kasar Amurka. A sakamakon haka, ana sa ran cewa, wadannan 'yan mata 2 na kasar Sin za su zama zakara a cikin gasa ta tsakanin mata biyu biyu ta budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Amurka da za a yi ba da dadewa ba.

An bude gasar fid da gwani ta wasan kwallo mai laushi ta mata ta kasa da kasa ta karo na 11 a nan Beijing a ran 27 ga wata. Kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyoyin kasashen Birtaniya da Italiya da Korea ta Arewa daya bayan daya. Nagatattun kungiyoyi 16 da suka hada da Amurka da Japan da Canada da Australia da sauran kungiyoyi 12 suna karawa da juna. Za a kammala dukan gasanni a ran 5 ga watan Satumba.

Ran 27 ga wata, a Saitama na kasar Japan, a cikin gasar neman shiga nagartattun kungiyoyi 8 ta gasar fid da gwani ta wasan kwallon kwando ta maza ta kasa da kasa da aka yi, kungiyar kasar Sin ta sha kaye daga hannun kungiyar kasar Grika da 64 da 95, shi ya sa ba ta shiga nagartattun kungiyoyi 8 a wannan gami ba. A cikin sauran gasanni 3 ma, kungiyoyin kasashen Amurka da Jamus da Faransa sun lashe kungiyoyin kasashen Australia da Nijeriya da kuma Angola daya bayan daya.(Tasallah)