A ran 29 ga wata a nan birnin Beijing, madam Susan Schwab, sabuwar wakiliyar Amurka wajen yin shawarwarin ciniki ta yi bayani inda ta nuna fatan kasar Sin za ta kara ba da babban taimako don sa kaimi ga sake yin shawarwarin ciniki na zagayen Doha.
A gun wani taron cin abin rana da aka yi a wannan rana, madam Schwab ta yi nadama ga abin da aka shelanta cewa za a tsayar da shawarwarin ciniki na zagayen Doha. Ta ce, sa kaimi ga samun nasarar karshe ga yin shawarwarin ya dace da moriyar mambobi daban-daban na kungiyar ciniki ta duniya, kasar Sin wata muhimmiyar mamba ce ta kungiyar, sabo da haka tana fatan kasar Sin za ta ba da babban taimako don sa kaimi ga sake yin shawarwarin ciniki na zagayen Doha.
|