Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-29 18:08:00    
Kasar Sin ta gama aikinta na aikawa da rundunar kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Kongo (Kinshasa) ta karo na 5 don maye gurbin sojojinta

cri
Bayan da rundunar kiyaye zaman lafiya ta karo na 5 ta kasar Sin ta kammala aikin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. na tsawon watanni 8 a kasar Kongo (Kinshasa), a ran 29 ga wata hafsoshi da mayaka 80 na kasar Sin da suka yi saura a can sun sauko nan birnin Beijing cikin jirgin sama na musamman, wannan ya alamanta cewa, Kasar Sin ta samu nasara wajen aikawa da rundunar kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Kongo (Kinshasa) cikin kashi 5 don maye gurbin sojojinta.

Tun watan Afrilu na shekarar 2003 zuwa yanzu, bisa rokon da M.D.D. ta ya mata ne, kasar Sin ta aika da rundunar kiyaye zaman lafiya cikin kashi 5 zuwa kasar Kongo (Kinshasa) domin tafiyar da aikin kiyaye zaman lafiya. Cikin shekaru 3 da 'yan kai da suka wuce, hafsoshi da mayaka na rundunar sun kammala ayyuka fiye da 100 da M.D.D. ta danka mata cikin nasara, ciki har da gina barikokin soja da filayen jiragen sama da filayen yaki da rushe makamai da harsasai, hafsoshi da mayaka 875 na rundunar dukkansu sun sumu lambobin yabo na kiyaye zaman lafiya na M.D.D. (Umaru)