Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-29 17:55:19    
Dangantakar cinikayya da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ta samu cigaba sosai

cri

Shekarar 2006 shekara ce da cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Dangantakar cinikayya da ke tsakaninsu ma ta samu cigaba sosai a cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce. A shekarar bara, yawan kudin cinikayya da aka samu a tsakaninsu ya kai kudin dolar Amurka biliyan 39.74, wato ya ninka fiye da sau 8 a cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce.

A cikin rabin karnin da ya gabata, cinikayyar da aka yi a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta samu cigaba cikin sauri sosai. Musamman tun daga shekara ta 2001, saurin bunkasuwar cinikayyar da aka yi a tsakaninsu ya kai kashi 40 cikin kashi dari a kowace shekara. Wannan ya bayyana cewa, dangantakar cinikayya da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka tana da makoma da dama sosai.

San nan kuma, ingancin kayayyakin da ake ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka yana ta samun kyautatuwa. Da farko dai, an yi ta kyautata tsarin kayayyakin da ake ciniki a tsakaninsu. A farkon lokaci, an yi cinikin auduga da amfanin gona da albarkatun ma'adinai. Daga baya, an yi cinikin kayayyakin sassaka da wasu kayayyakin masana'antu. Amma yanzu, yawancin kayayyakin da ake ciniki a tsakaninsu kayayyakin da ke da fasahohin zamanni da injunan lantarki na zamani.

Bugu da kari kuma, yanzu ana yin ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta hanyoyi iri iri. A farkon lokaci, ana yin ciniki a tsakanin jama'ar su kawai. Amma yanzu, ba ma kawai ana yin ciniki a tsakaninsu ba, har ma ana yin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannonin zuba jari da neman kwangilolin gina ayyukan yau da kullum da ba da taimako a kan wasu ayyukan yau da kullum. A karnin 50 da na 60 da suka gabata, ana yin cinikin waje a tsakanin Sin da kasashen Masar da Morocco da Tunisiya kawai, amma yanzu ana yin ciniki a tsakanin Sin da dukkan kasashen Afirka. Ya zuwa shekarar bara, kasashen Afirka da suka shigar da kayayyaki daga kasar Sin da darajarsu ta kai dolar Amurka fiye da miliyan dari 1 a kowace shekara sun kai 26. A sa'i daya kuma, kasashen Afirka da suke fitar da kayayyakinsu zuwa nan kasar Sin da darajarsu ta kai dalar Amurka fiye da miliyan dari 1 a kowace shekara sun kai 18.

Bayan shigowarmu a karni na 21 da muke ciki, dangantakar cinikayya da ke kasancewa a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta fi samun karfafuwa, kuma ta fi samun cigaba. Ingancin irin wannan dangantaka ma yana ta samun kyautatuwa. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta kulla dangantakar cinikayya a kasashen Afirka fiye da 50, kuma ta kulla "Yarjejeniyar cinikayya a tsakanin bangarori biyu" a tsakaninta da kasashen Afirka fiye da 40 yayin taka kafa hadaddun kwamitocin tattalin arziki da cinikayya da kasashe 35. Bugu da kari kuma, ta kulla "Yarjejeniyar sa kaimi da tabbatar da yunkurin zuba jari a tsakanin bangarori 2" da kasashen Afirka 28 da dai makamatansu.

Ban da wadannan, tun daga shekara ta 2005, kasar Sin ta tsai da kudurin cewa, za ta soke harajin kwastam ga ire-iren kayayyaki 190 da ake shigo da su a kasar daga kasashen Afirka 29 wadanda suke fama da talauci kwarai. Yawancin wadannan kayayyaki 190 kayayyaki ne da kasashen Afirka suke fitar da su zuwa kasashen waje sosai. Tabbas ne irin wadannan yarjejeniyoyi da tsare-tsare kuma da manufofin da suke amfanar juna suna bayar da gudummawa sosai ga bunkasuwar cinikayya a tsakanin Sin da kasashen Afirka cikin hali mai dorewa.

Ana cike da imani cewa, kasashen Sin da Afirka sun samu sakamako sosai wajen cinikayya domin sun yin hadin guiwa sosai a tsakaninsu a cikin shekaru 50 da suka wuce. Ko shakka babu, bangarorin Sin da kasashen Afirka za su kara ciyar da irin wannan dangantakar cinikayya gaba, kuma tana da makoma mai haske kwarai. (Sanusi Chen)