Assalamu alaikun. Jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka. A wannan mao ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan kasuwar kasa da kasa mai suna Tangga da ke gundumar Pulan ta yankin Ali na jihar Tibet ta kasar Sin, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, ziyarar kogunan dutse na Longyou.
An mayar da kasuwar kasa da kasa ta Tangga a matsayin kasuwar kasa da kasa da ta fi tsayi daga leburin teku a duniya, da can mutane su kan sayi abubuwa da abubuwan da suke da su kai tsaye ko kuma a fakaice a lokacin ciniki. Yanzu mutane iri daban daban suna ci gaba da yin ciniki a nan.
Bisa abubuwan da aka rubuta a cikin littattafai, an ce, mutane sun yi shekaru misalin dari 5 suna yin ciniki a bakin iyaka a gundumar Pulan. An kafa kasuwar kasa da kasa ta Tangga a gangaren tudu mai suna Dalaka da ke arewa maso yammacin kogin Kongque, akwai koguna da yawa a gindin wannan tudu, an ce, 'yan kasuwa na kasashen Indiya da Nepal ne suka haka wadannan koguna don kwana a ciki yau da shekaru daruruka da suka wuce. Saboda 'yan kasuwar kasar Nepal sun sami rinjaye a nan, shi ya sa ake kiran wannan wuri 'babban gini na 'yan kasar Nepal'.
Kasuwar Tangga kasuwa ce inda 'yan kasuwa na kasashen Indiya da Nepal da wasu 'yan kabilar Zang na wurin suke yin ciniki. An shimfida gadoji guda 2 zuwa kasuwar Tangga, shi ya sa an samu wata karamar kasuwa a wurin da ke tsakanin tsohon birnin da gadojin, inda kananan 'yan kasuwa na kasar Sin da wasu 'yan kasar Nepal suke yin ciniki. Kogi ya raba kasuwar Tangga sassa 2, wata a gabar kogin ta gabas, wata daban a gabar kogin ta yamma, nisan da ke tsakaninsu ya kai misalin kilomita 3.
'Yan kasuwa na kasashen Indiya da Nepal suna yin cinikin yadi da zanen gado da sukari mai launin ja da turare na kasar Faransa da na kasar Indiya da man da mutane suke yi amfani da shi a kai da kayayyakin shafa da kayayyakin ado da dai sauransu. Wasu daga cikinsu kuma suna yin musayar ulu da sauran kayayyaki daga hannun mutanen wurin da sukari mai launin ja da kayayyakin masarufi.
An bude kasuwar kasa da kasa ta Tangga tun daga ran 15 ga watan Yuli zuwa ran 15 ga watan Oktoba na ko wace shekara.
To, jama'a masu sauraro. Muna muku godiya da saurarenmu, kuma muna fatan za ku ci gaba da sauraren shirin nan na yawon shakatawa a kasar Sin, bari mu kai ziyara ga kogunan dutse da ke gundumar Longyou ta lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin.
|