Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-29 17:00:09    
Yin wasan yoga zai ba da taimako ga masu kamu da ciwon sankara

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani cewa, yin wasan yoga zai ba da taimako ga masu fama da ciwon sankara, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka: Za a karfafa hadin gwiwa kan ba da agaji bayan aukuwar girgizar kasa a shiyyar Asiya da tekun Pacific. To, yanzu ga bayanin

Bisa samakamakon farko na nazari da aka bayar a kasar Amurka, an ce, idan mutanen da suka kamu da ciwon sankarar mama suka yi wasan yoga yayin da ake yin musu jiyya ta hanyar magani ta yin amfani da haske, to za a ba da taimako ga lafiyar jikinsu.

Kwararrun cibiyar binciken ciwon sankara ta Anderson ta jami'ar Texas ta kasar Amurka sun bayar da wannan sakamako ne a gun taron shekara-shekara na kungiyar ciwon sankara ta Amurka a ran 4 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki. Manazarta sun nemi mata 62 da suke kamu da ciwon sankarar mama wadanda ake yin musu jiyya ta hanyar magani ta yin amfani da haske bayan da aka yi musu tiyata, kuma an raba wadannan mata da matsakaicin shekarunsu ya kai 52 da haihuwa cikin kungiyoyi biyu. Matan da ke cikin wata kungiya sun yi wasan yoga sau biyu a ko wane mako, sauran matan da ke cikin kungiyar daban ba su yi wasan yoga ba.

Bayan makwanni shida, manazarta sun gano cewa, jikin mata da suka yi wasan yoga jikinsu sun sami sauki, kwarewarsu wajen yawo da hau matakalu da dauki abin nauyi sun fi kyau idan an kwatanta su da na kungiyar daban. Wasu matan da suka kamu da ciwon sankarar mama sun bayyana cewa, bayan da suka yi wasan yoga, ba su ji gajiya sosai ba, kuma sun iya barci da kyau.

Makasudin yin wasan yoga shi ne karfafa tankwaruwar masu yin wasan ta yin motsi sannu sannu, kuma su samu sakin jiki ta kyautata numfashinsu. Darusan wasan yoga da manazarta suka shirya suna da sauki a gwargwado, ta yadda mata da ke fama da ciwo ba za su sha wahalar yin wasan yoga ba. Kuma manazarta sun bayyana cewa, za su ci gaba da yin bincike domin tabbatar da cewa, dalilin da ya sa mata masu fama da ciwon sankarar mama suka sami sauki shi ne domin wasan yoga ko amfanin hakalin mutane.