Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-29 16:40:52    
Yin yawon shakatawa a kogunan dutse na Longyou

cri

A gundumar Longyou da ke lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin, akwai wasu kattan kogunan dutse a karkashin kasa, wadanda ke jawo sha'awar masana, har ma masu yawon shakatawa da yawa su kan ziyarce su. A cikin shirinmu na yau, bari mu ziyarci wadannan kogunan dutse na Longyou masu ban mamaki.

Kogunan dutse na Longyou suna cikin wani kauye mai suna Shiyanbei da ke arewacin gundumar Longyou, an samu ruwa da bishiyoyi masu yawa a kewayensu. Da can mazaunan wurin sun gano 'yan tabkuna da yawa a cikin babban dutse, inda akwai ruwa mai tsabta sosai, kuma ba a iya isa karshen wadannan 'yan tabkuna ba. A cikin lokacin zafi na shekarar 1992, 'yan kauyen sun nemi yin ban ruwan da ke fitowa daga wadannan 'yan tabkuna, shi ya sa suka yi famfo ga wani karami daga cikinsu, sun yi kwanaki 17 suna ta yin famfo, a karshe dai sun tono wani babban dakin dutse a karkashin kasa, 'yan kauyen sun kara jin mamaki, saboda haka, sun yi famfo ga 'yan tabkuna 7 duka, a karshe sun tono kogunan dutse 7, wadanda suke zama kusa da juna, tsarinsu kusan duk daya ne, amma fadinsu sun sha bamban. Abin mamaki shi ne ba a samu tsoffin kayayyakin gargajiya a cikin dukan wadannan kogunan dutse 7 ba, sai wani mutum-mutumin dutse ba tare da kansa ba. Lokacin da yake zantawa da wakilinmu, ma'aikacin cibiyar aikin injiniya ta kasar Sin Mr. Wang Sijing ya bayyana cewa, 'yan kauyen Shiyanbei sun ji mamaki saboda tono wadannan kogunan dutse, amma ba su gano cewa, abubuwan da suka tono gine-gine ne mafi girma da 'yan Adam suka gina a karkashin kasa a duk duniya ba. Ya ce, 'lokacin da nake ziyararsu a karo na farko, na darajanta kakan kakanmu kwarai saboda sun gina wadannan dakunan dutse da ke karkashin kasa, da kyar muna zaton cewa, suna da fasaha da kwarewa na leburin koli kamar haka.'

Mr. Wang ya kara da cewa, ko wane kogon dutse wani babban daki ne na dutse, wanda fadinsa ya kai a kalla murabba'in mita dubu 1. Rufin ko wane dakin dutse ya tokare da kattan ginshikai a kalla 1, wasu kuma suna da 2 ko 3 ko kuma 4. Abin da ya fi ban mamaki shi ne an haka wadannan kogunan dutse bisa siffar taurarin Triones. Mataimakin darektan cibiyar ilmin kimiyyar dynam da aikin injiniya na dutse ta kasar Sin Mr. Yang Linde ya sha ziyarar kogunan dutse na Longyou. Ya yi bayanin cewa, bayan da muka yi bincike, mun gano cewa, an haka wadannan kogunan dutse ne bisa shirin gine-gine da aka tsara a tsanake, suna kusa da juna, amma ba su hada da juna ba, mutane na zamani sun ji mamaki sosai domin fasahar yin ma'auni a karkashin kasa ta yi daidai haka. Ya ce, (murya ta 2, Mr. Yang)

'duk lokacin da nake ziyarar kogunan dutse na Longyou, na kan ji farin ciki, kakan kakanmu masu fasaha ne suka haka wadannan kogunan dutse, wadanda suke amfanawa wajen bayyana tarihin al'adun gargajiya na kasar Sin.'

Ba safai a kan samu wani abu kamar irin na kogunan dutse na Longyou ba a duk duniya a fannonin girmansu da tsarinsu da zane-zanensu da fasahar gina su, da kuma ire-irensu. Ko da yake masana na kasar Sin sun yi bincike mai zurfi kan wadannan kogunan dutse daga fannoni daban daban, amma har zuwa yanzu ba su san su sosai ba, akwai tambayoyi da yawa da ba a iya amsa su ba, kamar su dalilin da ya sa aka haka wadannan kogunan dutse, da lokacin da aka haka su, da asalin mutanen da suka haka su, da hanyoyin da suka bi da abubuwan da suka yi amfani da su wajen haka su da dai makamantansu.

Masu yawon shakatawa dubu dubbai na gida da na waje sun ziyarci kogunan dutse na Longyou domin neman amsa tambayoyin da wadannan kogunan dutse suke samar da su. Madam Zhang Gu, wadda ta fito daga jihar Inner Mongolia da ke arewacin kasar Sin, ta ce, 'wannan yana da ban mamaki sosai, na zo nan ziyara ba don ina jin sha'awa kan wannan kawai ba, amma don ina girmama wannan nasarar da kakan kakanmu suka samu.'

Masu yawon shakatawa na kasashen wajen masu yawa su ma sun ziyarci kogunan dutse na Longyou saboda shahararsu. Madam Soili Vatanen, 'yar kasar Finland, ta gaya wa wakilinmu cewa, (murya ta 4, madam Vatanen)

'mun ziyarci kogunan dutse na Longyou a kwanan baya ba da dadewa ba, na ji mamaki kwarai, da can ban taba ganin irin wannan wuri ba, har ma ban san akwai irin wannan wuri a duniya ba, in kun sami damar ziyarar kasar Sin, tabbas ne sai ku kai ziyara ga kogunan dutse na Longyou.'