Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, ta bayar da taimako a zamani daban daban ga kasashen Afirka a fannoni daban, to, wannan ya sami yabo daga gwamnatocin kasashen Afirka da kuma jama'arsu, kuma wannan ya kara sa kaimi ga bangarorin biyu da su gama kai da taimakawa juna a ko wane hali da ake ciki.
A karshen shekarar 1963 zuwa farkon shekarar 1964, wato a yayin da firayin minstan kasar Sin na wancan lokaci Zhou Enlai yake ziyarar aiki a kasashe 10 na Afirka, Mr Zhou ya karfafa cewa, kasar Sin ta ba da taimako ga kasashen Afirka ba tare da ko wane irin sharadi ba kuma tana girmama mulkin kai na wadannan kasashe, har yanzu kasar Sin tana gudanar da wannan ka'ida.
A cikin shekaru 50 da 60 na karni da ya gabata, kasar Sin ta kan bayar da taimako ga kasashen Afirka ta hanyoyin gine-gine da kayayyaki da tura kwararru da dai sauransu. Bayan da kasar Sin ta fara gudanar da manufar yin gyare gyare a gida da bude kofa ga duniya a shekarar 1978, kasar Sin ta kara yawan hanyoyin bayar da taimako ga kasashen Afirka kamar ba da kyautar kudi da ba da rancen kudi ba tare da ruwa ba da horar da kwararru da kafa kamfanoni a kasashen Afirka da dai sauransu. Bangarorin biyu suna kara mai da hankali a kan ingancin gama kansu a fannin tattalin arziki da kara bunkasa dangantakar cinikayya da ke tsakaninsu da kara kyautata tsarin tabbatar da gudanar da yarjejeniyoyin da suka kulla. Abu na musamman shi ne, tun daga shekaru 90 na karni na 20, kasar Sin ta kara bayar da taimako ga kasashen Afirka a fannonin horar da kwararru masu fasaha da zuba jari domin kafa cibiyoyin cinikayya da sokewa ko rage basussuka da wasu kasashen Afirka suka ci daga wajenta da horar da jami'an tattalin arziki da cinikayya da ba da agaji domin yaki da bala'in halittu da dai sauransu.
Idan aka kwatanta taimakon da kasar Sin ta bayar da taimakon da sauran kasashe suka baiwa kasashen Afirka, sa'an nan za a ganin cewa, wani abu na musamman shi ne kasar Sin ta bayar da taimako ne da kyakkyawar aniya, ba ta nemi moriya ba, kuma ba ta sanya matsi a kan kasashen Afirka ba, kuma ba ta tsoma baki cikin harkokin gida na Afirka ba. Ban da wanna kuma, kasar Sin ta kan bayar da kayayyaki da kasashen Afirka suke bukata cikin gaggawa, amma sauran kasashe su kan bayar da kudi, sabo da haka, taimakon da kasar Sin ta bai wa kasashen Afirka ya kan sami kyakkyawan sakamako da kyau, a sakamakon haka, kasashen Afirka sun fi maraba ga taimakon da kasar Sin ta bayar. Tun daga shekarar 2003 zuwa yanzu, shugabanni na kasashen Madagascar da Eritrea da Ruwanda da dai sauran kasashen Afirka su kan nuna yabo da godiya ga taimakon da kasar Sin ta ba su, haka kuma ba su son taimakon da wasu kasashen yamma suka bayar tare da sharadi, wasu shugabanni kuma sun yi kira da kin karbar irin wannan taimako.
Shekarar da muke ciki shekara ta 50 da kasar Sin da kasashen Afirka suka raya dangantakar diplomasiyyarsu. A cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, taimakon da kasar Sin ta bayar ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin Afirka da kyautatta zaman rayuwar jama'arsu da kara daga matsayin ilimi da likitanci da kiwon lafiya da dai sauransu. Sabo da haka, bangarorin biyu suna kara amincewa da juna a kan tattalin arziki da siyasa. Kasashen Afirka sun nuna goyon baya ga kasar Sin a kan hakkin 'dan Adam da murkushe makircin Taiwan a MDD da shirya wasannin Olympics a shekarar 2008 da dai sauransu.(Danladi)
|