Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-29 14:23:43    
An bude taron kiwon lafiya na pan Afirka a karo na biyu

cri

A ran 29 ga wata, an bude taron kiwon lafiya na pan Afirka a karo na biyu a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, kuma za a rufe taron a ranar 31 ga wata. Babban take na wannan taro shi ne 'yadda ake amfani da kula da kudi a fannin kiwon lafiya', wannan ya zama wani muhimmin aikin da ke gaban shugabannin hukumomin kiwon lafiya.

Masu shirya taron kiwon lafiya sun karfafa cewa, nahiyar Afirka tana da wadatattun albarkatun tattalin arziki, amma idan ana son amfani da su, to, tilas ne kasashen Afirka su nemi isassun kudi domin tabbatar da lafiyar jama'a, haka kuma kudin taimako da sauran kasashe suka bai wa Afirka suna da muhimmanci sosai ga shawo kan manyan cututtuka biyu, wato tarin huka da cutar kanjamau. Bisa rahoton da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta bayar a shekarar 2006, an ce, wani abu mai ban tsoro shi ne, ko da yake za a iya shawo kan tarin huka, amma ba hakan bai samu ba a nahiyar Afirka ba. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a shekarar 1990, yawan 'yan Afirka da suka kamu da tarin huka ya zarce miliyan daya da dubu 600, a shekarar 2004 kuwa, yawansu ya zarce miliyan uku da dubu 374, haka kuma a shekarar 1990, yawan mutane da suka mutu a sakamakon tarin hufa ya kai dubu 200, amma a shekarar 2004, yawansu ya karu zuwa dubu 587. Cutar kanjamau kuwa ita ce ta fi tsanani a kasashen Afirka. Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kimanta cewa, yawancin mutane da ke kamuwa da cutar kanjamau, 'yan shekaru 15 zuwa 49 da haihuwa ne, suna zama a kasashe da ke kudancin Afirka. Ko da yake ana samun ingantuwar matsalar cutar kanjamau a sauran kasashen Afirka, amma yanzu akwai matsala. Sabo da haka ne, yadda za a sami kudade domin aikin kiwon lafiya a Afirka, kuma yadda za a amfani da su da kuma yadda za a kula da su, ya zama wata matsalar da za a takara cikin gaggawa.

Sabo da haka ne, a gun taron kiwon lafiya na kwanaki uku, hukumomin kiwon lafiya da jin dadin yara da kungiyoyi da ba na gwamnati ba da dai sauran hukumomin kasashen Afirka, za su yi bincike da bayar da jawabai domin tattaunawa a kan yadda za a yi amfani da kudaden kiwon lafiya, musamman kudin taimako da kasashen duniya suka bayarwa.

Bisa labarin da muka samu, an ce, za a tattauna a kan fannoni uku, na daya, yadda masu ba da kudin taimako da kamfanoni da hukumomi da gwamnatoci da abin ya shafa da su kafa wani tsari mai inganci na kiwon lafiya.

Na biyu, za a tattauna a kan mugun illar da cutar tarin huka da cutar kanjamau suke haifuwa ga kamfanoni da ma'aikatansu, kuma yadda za a dauki matakai domin kawar da irin wannan illa.

Na uku, yadda za a bayar da dama ga hukumomin da ba na gwamnati ba domin su kara taka muhimmiyar rawa a fannin kiwon lafiyar jama'a.

Ban da wannan kuma, wakilan da suka zo daga bankin duniya da hukumomin kiwon lafiya da jin dadin yara na Afirka za su tattauna a kan nauyin da ke bisa wuyan gwamnatocin kasashen Afirka dangane da yadda suke amfani da kudaden kiwon lafiya.

A gun taron kuma, za a shirya bikin nune-nunen kayayyakin kiwon lafiya da kasashen Afirka suka yi. Haka kuma za a shirya wani dandalin tattaunawa domin masu sayar da kayayyaki da masu sayen kayayyaki su yi musanyar ra'ayoyinsu, ta yadda za a kafa wata kyakkyawar dangantaka tsakaninsu.

Haka kuma, a gun wannan taron kiwon lafiya na pan Afirka a karo na biyu, za a bayar da kyaututtukan yabo ga mutane wadanda suke aiki da kyau da wadanda suke yin kirkire-kirkire sosai a fannin kiwon lafiya a nahiyar Afirka.(Danladi)