Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 22:32:28    
An bude taron kasa da kasa na shekara ta 2006 dangane da rage bala'i

cri
A yau ranar 28 ga wata, a birnin Davos na kasar Switzerland, an bude taron kasa da kasa na shekara ta 2006 a kan batun rage bala'i, kuma hukumar kula da rage bala'i ta MDD da kuma kungiyar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD, wato UNESCO, su ne suka hada kai suka shirya taron. Mahalartan taron za su tattauna bala'i iri daban daban da ake fuskanta a duniyar yau, kuma za su yi musanyar ra'ayoyi a kan matakai masu amfani da za a dauka.

A gun bikin bude taron, shugaban taron, Walter Ammann ya ce, ana fuskantar bala'i iri iri a duniyar yau. A cikin irin wannan hali ne, tilas ne a fitar da wani sabon ra'ayi dangane da yadda za a kula da bala'in, ta yadda za a rage hadari mafi gaggawa da ke gaban duniya. Ya kara da cewa, babban makasudin wannan taro shi ne nuna hadarurruka iri iri da suka fi daukar hankulan mutane, kuma a tattauna su, ta yadda za a samu hanyar da za a bi don daidaita matsalar cikin dogon lokaci.(Lubabatu)