Cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta mai da aikin hana aukuwar hadarurrukan mahakan kwal ya zama aikin farko domin aikin kawo albarka cikin lumana.
Kwanan baya kasar Sin ta tsara shirin aikin kawo albarka cikin lumana na shekaru 5 masu zuwa, wanda a ciki aka jaddada cewa, cikin shekaru 5 masu zuwa kasar Sin za ta yi namijin kokari domin hana aukuwar manyan hadarurrukan mahakan kwal, kuma za a yi kokarin shafe shekaru 3 domin daidaita matsalolin rashin samun sharuda masu kyau wajen aikin kawo albarka na kananan mahakan kwal, sabo da haka an yi hadarurruka da yawa. Kuma za a dauki matakai don sa ido kan mafarin manyan hadarurruka da daidaita manyan rikice-rikecen da ke kwance, da kafa tsarin share fage don sa ido da sarrafa mafarin manyan hadarurruka, da kara saurin kafa da kuma kyautata dokokin aikin kawo albarka cikin lumana. (Umaru
|