Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 21:20:18    
Kasar Sin za ta kara inganta hadin gwiwar da ke tsakaninta da sauran kasashen duniya wajen zirga-zirgar samaniya

cri
A ran 28 ga wata, Mr. Jin Zhuanglong, mataimakin direktan kwamitin masana'antar kimiyya da fasaha ta tsaron kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara inganta hadin gwiwar da ke tsakaninta da sauran kasashen duniya wajen zirga-zirgar samaniya, kuma za ta yi kokarin fitar da kayayyaki da yin hidima zuwa kasashen waje a wannan fanni.

Mr. Jin Zhuanglong ya bayyana cewa, cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za kara rubanya kokari don sa kaimi ga hadin gwiwar da ake yi a tsakaninta da Rasha da Ukraine wajen fasahar zirga-zirgar samaniya, da inganta hadin gwiwar da ke tsakaninta da kasashen Turai wajen zirga-zirgar samaniya, da sa kaimi ga yin hakikanin hadin gwiwa a tsakaninta da Amurka da Canada wajen kafa hukumomin samaniya. Ban da wannan kuma za ta ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakaninta da M.D.D. da sauran kungiyoyin kasashen duniya, da kafa cibiyar ba da ilmi da yin horo ta Asiya da shiyyar tekun Pasific ta M.D.D. kan kimiyya da fasahar samaniya. (Umaru