Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 18:00:36    
Kasar Sin tana kokarin yin hadin guiwar kasashen duniya wajen yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana

cri
Kasar Sin tana kokari sosai wajen yin hadin guiwar kasashen duniya domin yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana. Ya zuwa yanzu, yawan yarjejeniyoyi da takardun kasa da kasa na makamashin nukiliya da hukumar makamashin nukiliya ta kasar Sin ta kulla ya riga ya kai 70, yawan ayyukan ba da taimakon hadin guiwar fasaha da take yi ya kai 54. Yanzu kasar Sin tana ta bayar da muhimmiyar gudummawa wajen hana yaduwar nukiliya da yin amfani da makamashin nukiliya da fasahar nukiliya cikin lumana.

Wakilinmu ya samu wannan labari ne a gun wani taron da aka yi a birnin Beijing a ran 28 ga wata.

An bayyana cewa, daya bayan daya ne kasar Sin ta riga ta kafa tsarin mu'ammala da juna a tsakanin ministocinta da kasashen Faransa da Japan kuma da na kasar Koriya ta kudu. Sun kuma kafa tsare-tsaren yin wannan aiki a karkashin jagorancin gwamnati. San nan kuma, tashar samar da wutar lantarki da makamashin nukiliya ta Chashma da kasar Sin da kasar Pakistan suka gina tare yanzu ta shiga mataki na 2 lami lafiya. (Sanusi Chen)