Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 19:44:45    
Masu aikin sa kai na kasar Sin sun nuna sahihiyar zuciya ga Nahiyar Afrika

cri

Tun daga shekarar 2002 ne aka soma gudanar da shirin hidima ga kasashen ketare da samari masu aikin sa kai na kasar Sin suka yi, wadanda aka karbe su ta hanyar yin rajista bisa son kai. Samari masu aikin sa kai na kasar Sin sun shiga cikin Nahiyar Afrika ne a shekarar 2005 a karo na farko, sun sa kafa a kasar Habasha. To, yaya zaman rayuwarsu a can? Kuma wane irin tasiri ne da suka kawo wa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Afrika? To, yanzu bari mu dan gutsura muku wani labari game da wannan lamari.

Alamar yunkurin samari masu aikin sa kai na kasar Sin, ita ce wani hannu mai siffar zuciya, wanda yake bayyana yadda ake mika hannu domin taimakon mutane wadanda suke bukatar samun taimako. Samari masu aikin sa kai na kasar Sin ba ma kawai sun gudanar da harkokin hidima a cikin gidan kasar ba, har ma sun mika hannunsu domin taimakon jama'ar kasashen duniya.

A ran 4 ga watan Agusta na shekarar bara, samari masu aikin sa kai su 12 daga birnin Beijing, da birnin Shanghai, da birnin Chengdu da kuma lardin Yunnan na kasar Sin sun je can Nahiar Afrika mai nisa cike da kyakkyawan burinsu domin yin aikin hidima na tsawon watanni 6 a kasar Habasha, inda suka bauta wa jama'ar Habasha da zuciya daya a fannin yin amfani da gas, da yin aikin koyarwa da Sinanci, da yin wasannin motsa jiki, da aikin jiyya da na tsabta da kuma samun labarai game da fasahohi da dai sauran fannoni.

A cikin rabin shekara da wadannan samari masu aikin sa kai na kasar Sin suka shafe suna zama a kasar Habasha, sun ganam ma idonsu yadda jama'ar Nahiyar Afrika suke shan wahala a cikin zaman rayuwarsu. Wadannan samari sun nuna sahihiyar zuciya ga jama'ar wurin, sun sanya matukar kokari wajen kyautata zaman rayuwarsu. Alal misali: sun yi aikin jiyya dake da sigar musamman na kasar Sin wato yin allurar gargajiya ta akufanca ga marasa lafiya na wurin; Ban da wannan kuma, sun bude kwas din koyon fasahar samar da gas domin amfanin jama'a, da ba da jagoranci ga 'yan makaranta domin yin gwaje-gwaje a fannin noma; Kazalika, sun horar da ma'aikatan hukumomin gwamnatin kasar da kuma sabon jakadan kasar da zai yi wakilci a kasar Sin cikin Sinanci.

A cikin lokacin hutu na bayan aiki, wadannan samari masu aikin sa kai na kasar Sin sun rubuta wakoki da kuma wassu kalmomi a cikin littafin tsarin lokaci, inda suka rubuta abubuwan da suka ji a cikin zukatansu da wadanda suka ganam ma idonsu. Wani saurayi ya rubuta wani bayanin, cewa abun tausayi, shi ne matsakaicin tsawon ran ko wane dan Habasha bai kai shekaru 55 da haihuwa ba saboda talauci da cututtuka.

Ayyukan da samari masu aikin sa kai na kasar Sin suka yi da kuma sahihiyar zuciya da suka nuna sun samu karbuwa sosai daga wajen jama'ar wurin. Bangarorin biyu sun kulla zurfaffen aminci da ba za su manta da shi ba har abadin abada. Bugu da kari kuma, samari masu aikin sa kai na kasar Sin su ma sun kara fahimtar ra'ayi mai tsarki na sa kai dake bauta wa jama'ar duk duniya ; Dadin dadawa, sun kara gano manufar girmansu ta nan gaba. Bayan da suka kammala aikin hidima na watanni 6 a kasar Habasha, wassu daga cikinsu kuma sun gabatar da rokonsu na ci gaba da yin aiki na tsawon watanni 6 a wannan kasa.

Wassu kwararrun da abun ya shafa na kasar Sin sun yi hasashen, cewa samari masu aikin sa kai na kasar Sin sun zama tamkar wata gada ce da hada kasashen Sin da Habasha domin yin musanye-musanyen sada zumunta ; Haka kuma sun kasance kamar wata tuta ce dake siffanta yadda samari da jama'a na kasar Sin suka nuna wa jama'ar Nabiyar Afrika kyakkyawan aminci.

Yanzu, rukunin farko na samari masu aikin sa kai na kasar Sin sun rigaya sun dawo na kasar mahaifa tare da nasara. Rukuni na biyu da na uku na samarin za su je Nahiyar Afrika daya bayan daya domin haye gurbin sha'anin sa kai na yin hidima ga jama'ar Afrika. Abun da ya fi faranta ran mutane, shi ne ana ta kara samun samari masu aikin sa kai na kasar Sin wadanda suke kishin yin hidima ga kasashen ketare. Wadannan samari sun lashi takobin ba da taimako gwargwadon iyawa ga sha'anin zaman lafiya da yunkurin raya kasa na bil adama. Mun yi imanin, cewa wata rana tutar nuna sahihiyar zuciya za ta karkata a Nahiyar Afrika da kuma sauran yankunan duniya, inda ake bukatar samun taimako. (Sani Wang)