Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-28 18:39:30    
Kasar Sin za ta mai da babban karfi wajen dudduba halin yadda ake tafiyar da dokokin aikin gona

cri
Hukumar mulkin kasar Sin wato zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa zai dudduba yadda ake tafiyar da dokoki 3 da suka shafi aikin gona, ta yadda za a sa kaimi ga daidaita matsalar rishin ci gaba da kiki-kaka wajen bunkasa kauyukan kasar Sin.

Wadannan dokoki 3 su ne, "Dokar sha'anin noma" da "Dokar sarrafa yankunan kasa" da kuma "Dokar dora nauyin aiki kan yankunan kauyuka ta hanyar yin kwangila". Cikin shekaru 3 da suka wuce, kasar Sin ta taba dudduba yadda ake tafiyar da wadannan dokoki 3, bayan dubawar da aka yi an ba da ra'ayoyi kan yadda za a tabbatar da manufofin kasar kan sha'anin noma da kara ba da kudin taimako ga bunkasa sha'anin noma. Makasudin dubawar a wannan gami shi ne domin kara karfin bunkasa aikin gona daga duk fannoni, da yin gyare-gyaren tsarin raya aikin gona ta hanyar kimiyya da fasaha, da kafa tsarin sarrafa yankunan kasa da kuma kiyaye gonaki cikin dogon lokaci, da kayutata ajandun karbar gonaki da tsarin ba da kudin rangwame. (Umaru)