 A ran 28 ga wata, an sami labarin kunar bakin wake cikin mota a bakin kofar babban ginin ma'aikatar harkokin gida ta kasar Iraki da ke tsakiyar birnin Baghdaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 14, kuma ya ji wa kusan mutane 40 raunuka.
Hukumar 'yan sanda ta kasar Iraki ta bayyana cewa, wajen karfe 10 da minti 45 na safiyar wannan rana, wani ya kai farmaki ya tuka wata mota don yin kokarin shiga cikin kofar babban ginin ta ma'aikatar harkokin gida ta Iraki, bayan da aka hana shi sabo da kangiyar sumunti da aka gitta a bakin kofar, sai mai ta da farmakin ya fasa bamaboman da ke cikin motar, wanda kuma ya haddasa mutuwar mutane da yawa ko ji wa wasu rauni. (Umaru)
|