Daga ran 5 zuwa ran 7 ga watan Agusta, kungiyoyin ba da agaji 17 da suka zo daga kasashe na shiyyar Asiya da tekun Pacific sun shiga gwajin ba da agaji bayan aukuwar girgizar kasa da aka shirya a birnin Shi Jiazhuan da ke arewacin kasar Sin, ta yadda za a karfafa kwarewar hadin kai da daidaituwa tsakanin kungiyoyin ba da agaji daban daban. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan gwajin nan.
Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD shi ne ya shirya wannan gwajin ba da agaji bayan aukuwar girgizar kasa. Kuma kafin wannan, an riga an shirya irin wannan gwaji har sau uku, amma wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta dauki nauyin shirya gwajin wanda kungiyoyin ba da agaji masu yawa na shiyyar Asiya da tekun Pacific suka shiga.
Tun ran 5 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, a karkashin taimakon da jami'an MDD suka bayar, kungiyoyin ba da agaji 17 da suka zo daga kasashen Sin da Japan da Amurka da Australia da Philippines da Korea ta Kudu da Indiya da dai sauran kasashe suka kwaikwayi yadda za a gudanar da ayyukan ba da agaji a wuraren da suka gamu da girgizar kasa mai tsanani, kuma sun shafe kwanaki uku suna yin wannan gwaji.
Jami'in ofishin kula da harkokin jin kai na MDD Arjun Katoch ya bayyana cewa, an cimma makasudin da aka tsara a da a cikin gwajin.
"gwajin na kwanaki uku wani zarafi ne mai daraja sosai gare mu. A cikin wannan lokacin, muka nazari matsaloli iri iri da za mu fuskantar a cikin bala'i, kamar hadin kai da aikin sadarwa da matsalar harsuna da dai sauransu. Ina ganin cewa, an shirya gwajin da kyau kwarai da gaske, kuma gwajin ya samu nasara sosai."
Mataimakin shugaban hukumar kula da girgizar kasa ta kasar Sin Zhao Heping yana ganin cewa, kasar Sin wata kasa ce da ta kan gamu da bala'i daga indallahi, shi ya sa tana bukatar shiga cikin irin wannan gagarumin gwaji na kasashen duniya dangane da ba da agaji bayan aukuwar girgizar kasa.
"shirya gwajin ba da agaji bayan aukuwar girgizar kasa na shiyyar Asiya da tekun Pacific a nan kasar Sin za ta ba da taimako kan binciken hadin gwiwa da ke tsakanin sassan kula da al'amuran gaggawa na kasar Sin da kungiyoyin ceto da ba da agaji na kasashen duniya, da karfafa karfinta wajen tinkarar bala'i mai tsanani, da kuma koyon dabaru da fasahohi masu kyau na kungiyoyin ba da agaji na kasashen waje, ta yadda za a share fage ga tinkirar al'amuran da suka auku ba zato ba tsammani da kuma rage hasarorin da ake samu a cikin bala'i."
Kasar Sin kuwa ta aika da kungiyarta kan ba da agaji don shiga gwajin. Bisa bayanin da shugaban sashen ba da agaji cikin gaggawa bayan aukuwar girgizar kasa ta hukumar girgizar kasa ta kasar Sin Huang Jianfa ya yi, an ce, an kafa kungiyar ba da agaji ta kasar Sin a shekara ta 2001, kuma ta taba zuwa kasashen Iran da Indonesiya da Pakistan da dai sauran kasashe domin shiga ayyukan ba da agaji bayan aukuwar girgizar kasa. Kasar Sin tana fatan kungiyar za ta iya koyon darasi mai kyau daga kungiyoyin ba da agaji na kasashen waje ta gwajin, ta yadda za a karfafa kwarewarta wajen ba da agaji ga kasashen waje. "bala'i mai tsanani zai yi mumunar illa ga wata shiyyar ko kuma duk duniya baki daya. tabbas ne za mu ci gaba da karfafa irin wannan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin ba da agaji a nan gaba. Ba da dadewa ba za mu aikawa da 'yan kungiyar ba da agaji ta kasar Sin zuwa kasar Singapore don karbi horo a jere da aka yi musu, ban da wannan kuma za mu kafa wani sansanin horo kan ba da agaji bayan aukuwar bala'i na kasar Sin, da kuma gayyatar malamai daga kasashe waje da su zo kasar Sin don koyar da ilmi na wannan fanni. Bugu da kari kuma za mu samar da wasu darusan horon fasaha ga kasashe masu tasowa domin karfafa kwarewarsu wajen tinkirar al'amuran da suka auku ba zato ba tsammani. "
Haka kuma Peter Thomas, wani jami'in ofishin kula da harkokin jin kai na MDD da ya shiga gwajin, ya gaya wa wakilinmu cewa, a cikin shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da taimako da yawa wajen ayyukan ba da agaji ga kasashen waje. Kuma a cikin ayyukan ba da agaji masu yawa bayan aukuwar bala'i daga indallahi mai tsanani, da zarar bala'i ya faru, sai gwamnatin kasar Sin ta aika da kungiyar ba da agaji zuwa wuraren da ke fama da bala'in, sabo da haka ta ba da babbar gudummowa sosai kan ayyukan fama da bala'i.(Kande Gao)
|