Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kananan kabilun kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu gabatar muku da bayani kan kabilar Bao'an ta kasar Sin, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani a karkashin lakabi haka: Sulaiman Imin, furofesa na kabilar Uygur da wakokin da ya wallafa. To, yanzu ga bayanin.
An fi samun 'yan kabilar Bao'an a gudumar Jishishan mai cin gashin kai ta kasar Sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin ta karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Achang ya kai wajen dubu 16. 'yan kabilar suna yin amfani da harshen Bao'an, kuma yawancinsu suna iya magana da harshen kabilar Han.
Sabo da 'yan kabilar Bao'an suna da zamansu a gundumar Jishishan da ke bakin iyakacin jihohin Gansu da Qinghai na kasar Sin, kuma suna kusa da kogin Yellow River, shi ya sa ana iya samun ruwa da ciyayi masu kyau, kuma ya fi kyau an raya sha'anin noma da kiwon dabbobi. Amma kafin kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, 'yan jari hujja sun mallaki filaye, shi ya sa tattalin arzikin wurin bai samu bunkasuwa cikin sauri ba.
Bayan da aka kafa kasar Sin, 'yan kabilar Bao'an sun samu hakkin zaman daidai wa daida da kuma gudanar da harkoki da kansu. A cikin wadannan shekaru fiye da 50 da suka gabata, an yi sauye-sauye a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu na kabilar. Musamman ma bayan taro na uku na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka yi a cikin shekara ta 1978, an raya sha'anin noma da cinikayya cikin sauri kwarai da gaske, zaman jama'ar kabilar Bao'an yana ta samun kyautatuwa.
kabilar Bao'an tana da al'adun gargajiya iri daban daban. A kan bayyana tarihin kabilar da soyayyar da ke tsakanin maza da mata a cikin labarai da wakoki da almara da ke da farin jini sosai a tsakanin fararren hula na kabilar. Dukkan 'yan kabilar su gwanaye ne wajen rawa da waka.
'Yan kabilar Bao'an suna bin addinin Musulunci, kuma su 'yan rukunin Sunni ne. Kuma sabo da su musulmai ne, shi ya sa su kan ci naman sa da tunkiya kawai, ban da wannan kuma su kan ci alkama da masara. 'yan kabilar Bao'an su kan yi bukukuwa da yawa, ban da bikin sallar bazara na kasar Sin, su kan yi kusan dukkan bukukuwa ne bisa addinin Musulunci, kamar Karamar Salla da Babbar Salla da dai sauransu.
|