A ran 28 ga wata, kasar Sin ta sanar da sakamakon nazarin allurar rigakafin cutar murar tsuntsaye ta rukuni na farko da hukumar shawo kan cututtuka ta kasar Sin da sauran hukumomin da abin ya shafa suka yi, sakamakon ya ce, allurar tana amfani ga lafiyar jikin mutane.
An fara bincike a kan wannan allura ne daga ranar 22 ga watan Nuwamba na shekarar 2005. Sakamakon bincike ya bayyana cewa, mutane 120 da aka yi wa wannan allurar suna cikin koshin lafiya, to, wannan ya bayyana cewa, allurar tana da amfani ga lafiyar jikin mutane.
Bisa labarin da muka samu, an ce, hukumomin da abin ya shafa suna kokari sosai domin fara bincike a kan allurar rigakafin murar tsuntsaye ta rukuni na biyu.(Danladi)
|