|
Kasar Sin da Pakistan za su kai farmaki kan "karfufuka iri 3" wato ta'addanci da masu jawo baraka da masu ra'ayin ga-ni-kashe-ni ta hanyar hadin gwiwa. A ran 27 ga wata, hukumar ikon kasar Sin wato zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar ya yarda da yarjeniyoyin hadin gwiwa da abin ya shafa.
An daddale wannan yarjejeniyar hadin gwiwa ce a watan Afrilu na shekarar da ta wuce, a cikin yarjejeniyar, bangarorin 2 wato Sin da Pakistan sun tsai da ma'anar "karfufuka iri 3", da tabbatar da abubuwa game da ba wa juna taimako wajen fasaha da kayayyaki da rahotannin asiri. Gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa, yarda da wannan yarjejeniya da fara aiki da ita suna da amfani ga kara hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2 wajen yin adawa da ta'addanci da sa kaimi ga dangantakar aminci tsakanin kasashen 2 wato Sin da Pakistan. (Umaru)
|