Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-27 18:15:14    
Kasar Sin ta kafa tsarin sa ido kan iska mai kura da ke dab da yankunan kasa

cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar a ran 27 ga wata an ce, a gundumar Minqin na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin wato wani muhimmin mafarin iska mai kura na kasar, an kafa wani tsarin sa ido kan iska mai kura da ke dab da yankunan kasa, a karshen wannan shekara kuma za a fara yin amfani da muhimman kayayyakin duba yanayi don sa ido a daidai lokaci da aika da bayanai ta hanyar zamani.

Wannan ya zama tsari ne da masu binciken kimiyya na kasar Sin suka bincika da yin fasali da kuma kara shi, wanda kuma karo na farko ne ya sa ido da yin binciken dokokin tashin iska mai kura da ke dab da yankunan kasa. Tsarin nan kuma zai iya samun muhimman labarai game da iska mai kura, ta hanyar yin binciken bayanan da aka tattara da aika da su, masu binciken kimiyya za su iya sarrafa muhimman dokokin iska mai kura da ta tashi a wurin, ta yadda za su dauki matakai masu amfani don yin rigakafi da rage yawan wahalolin da iska mai kura ta jawo wa mutane. (Umaru)