A ranar Lahadi 27 ga wata, Zhang Xinfeng, mataimakin ministan tsaron zaman lafiyar kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin za ta kafa wani cikakken tsarin yin rigakafin shigowa da sufurin miyagun magunguna a kasar daga hanyoyin kasa da na teku da na jiragen sama kuma da na waya.
San nan kuma, kasar Sin za ta kara karfin yin yaki da miyagun magunguna, kuma za ta kara mai da hankali kan lardin Yunnan da ke makwabtaka da kasashen waje a kudu maso yammacin kasar Sin da jihar Xinjiang wadda ke makwabtaka da kasashen waje a arewa maso yammacin kasar Sin, inda masu laifuffuka suke shigar da miyagun magunguna a kasar Sin, domin hana shigowar miyagun magunguna a nan kasar Sin. Bugu da kari kuma, za a kara yin aikin farautar miyagun magunguna a yankunan da ke bakin teku a kudu maso gabashin kasar Sin.
A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar Sin za ta kara taimaka wa mutane wadanda suka taba shan miyagun magunguna, amma yanzu suke yunkurin daina shan miyagun magani kan yadda za su kara sa niyyar yanke dangantaka a tsakaninsu da miyagun magani. Daga karshe dai, kasar Sin za ta kara daukar matakai masu tsanani wajen yin yaki da laifuffukan da ke shafar miyagun magani. (Sanusi Chen)
|