Bisa labarin da wakilinmu ya aiko mana, an ce, hadaddiyar kungiyar wakilan muhimman kafofin watsa labaru na kasar Sin wadda ke yin ziyarar sada zumunta a tsakanin Sin da Rasha ta isa birnin Moscow na kasar Rasha a ran 26 ga wata da dare lami lafiya bayan da ta sha tafiye-tafiye har na tsawon kilomita dubu 15 a cikin kwanaki 33 da suka wuce. Wannan ya almantar cewa, kungiyar ta riga ta cimma nauyin tuka motoci da aka dora mata.
A ranar Asabar 26 ga wata da dare, motoci 13 na kungiyar manema labaru da ke yin ziyarar sada zumunta a tsakananin Sin da Rasha sun isa wata tashar bincike da ke waje da birnin Moscow. Jami'an ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Rasha suna jiransu. San nan kuma, a rakiyar motocin 'yan sadan na kasar Rasha, motocin kungiyar sun shiga birnin Moscow kuma sun isa ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Rasha da karfe 8 da dare lami lafiya. Bayan saukarsu daga motoci, manema labaru sun yi musafaha kuma sun yi runguma da juna bi da bi domin taya murnar wannan lokacin da suke da wuyar manta da shi. (Sanusi Chen)
|