Ran 27 ga wata, babban wakilin kasar Iran Mr. Ali Larijani, wanda ke kula da shawarwarin nukiliya, ya bayyana cewa, kasar Iran za ta ci gaba da samar da makamashin nukiliya, saboda samar da makamashin nukiliya makasudi ne da kasar Iran ta tsara a fannin muhimman tsare-tsare.
Bisa labarin da gidan rediyon kasar Iran ya bayar, an ce, a ran nan Mr. Larijani ya yi bayanin cewa, samar da makamashin nukiliya makasudi ne da kasar Iran ta tsara a fannin muhimman tsare-tsare. Dukan matakan da aka dauka don yunkurin kwace iko daga hannun kasar Iran ba su iya tilasta mata canja makasudin da ta tsara a da ba. Kasar Iran ba za ta durkusa a gaban dukan matsin lamba daga kasashen waje ba, ba za ta yi watsi da shirinta na nukiliya ba.
A wannan rana kuma, a birnin Tehran, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Iran Mr. Hamid-Reza Asefi ya yi wa kafofin yada labaru cewa, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Mr. Kofi Annan zai kai wa kasar Iran ziyara a ran 2 ga watan Satumba, zai yi tattaunawa da kasar Iran kan batun nukiliya nata da halin da Gabas ta Tsakiya ke ciki.(Tasallah)
|