|
A ran 26 ga wata, yayin da mutanen kasashen waje wadanda suke kallon rawar daji da aka yi tsakanin Sin da Kazakhstan don yin adawa da ta'addanci sun amsa tambayoyin da manema labaru suka yi musu, sun yi yabo sosai ga wannan rawar daji ta karo na farko da aka yi tsakanin sassan tafiyar da dokoki da kiyaye kwanciyar hankali na kasar Sin da kasashen waje don yin adawa da ta'addanci.
Bosko Fladimir Karpovich, mataimakin shugaba na farko na kwamitin tsaron kasar Kazakhstan ya bayyana cewa, sassan kula da zaman lafiya da tsaron iyakar kasa na kasar Sin sun nuna nagartattun halaye da fasahar yaki sosai cikin yakin da suka yi da 'yan ta'adda, domin kai farmaki kan ta'addanci, ya kamata Sin da Kazakhstan su dinga yin hadin gwiwa domin kara yin binciken sabbin muhimman tsare-tsare da dabarun yaki don kai farmaki kan ta'addanci.
Vyacheslav Kasimov, direktan kwamitin zartarwa na hukumar yin adawa da ta'addanci ta kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ya ce, bayan da ya yi musanyar ra'ayoyinsa da 'yan kungiyar masu kallon rawar daji, 'yan kungiyar sun nuna babban yabo ga fasahar yaki da hafsoshi da mayaka suka nuna cikin rawar daji da makamai irin na zamani da suka yi amfani da su. (Umaru)
|