Ran 26 ga wata, Malam Meng Hongwei, shugaban hukumar yaki da ta'addanci na yankin kungiyar hadin kan Shanghai kuma mataimakin ministan tsaron jama'a ta kasar Sin ya bayyana a birnin Yining na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin cewa, ko da yake a galibi dai halin da ake ciki a kasashen kungiyar hadin kan Shanghai game da zaman lafiya yana tafiya yadda ya kamata, amma ya zuwa yanzu, ana fuskantar kalubale mai tsanani wajen yaki da ta'addanci a yankin.
A wannan rana da safe, kasar Sin ta yi atisaye mai lambar Tianshan ?1 a birnin Yining, wato atisayen hadin guiwa na zagaye na biyu da ake yi a tsakanin kasashen Sin da Kazakhstan don yaki da ta'addanci. Malam Meng Hongwei ya yi wannan furuci ne a wurin atisayen nan.
Ya kuma kara da cewa, ya zuwa yanzu, 'yan ta'adda da 'yan a-ware da kuma masu tsattsauran ra'ayi suna gudanar da harkokinsu ba ji ba gani a yankin kungiyar hadin kan Shanghai, sa'an nan kuma ana ci gaba da yin laifuffukan fataucin miyagun kwayoyi masu yawa cikin kungiya-kungiya kuma a tsakanin kasa da kasa, sabo da haka inganta hadin kai a fannin tsaro da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali wata mummunar dawainiya ce ga kungiyar hadin kan Shanghai a cikin wani tsawon lokaci. (Halilu)
|