Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-26 20:39:14    
Kasar Iran ta bayyana cewa, ta sami sabon sakamako wajen yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana

cri

A ran 26 ga wannan wata a gun bikin kammala da kuma soma aiki da ma'aikatar inganta ruwa wato Heavy Water da ke garin Khondab na tsakiyar kasar Iran, shguaban kasar Iran  Mohmoud Ahmadinejad ya bayyana cewa, jama'ar Iran za su kare hakkinsu na raya fasahar nukiliya ta han yar yin amfani da makamai.

A ran 25 ga wannan wata, kakakin gwamnatin kasar Iran Gholam Hossein Elham ya bayyana cewa, kasar Iran ta riga ta sami sabon sakamako wa jen yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, kuma za ta sanar da labarin da abin ya shafa ba da dadewa ba.

A wannan rana, wakilin kasar Iran da ke wakilci a hukumar makamashin nukiliya ta kasashen duniya Ali Asghar Soltainyeh ya bayyana cewa, kasar Iran ba ta taba hana masu yin bincike na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wajen yin bincike kan ayyukan nukiliya na kasar ba, yanzu, masu bincike na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa suna nan suna kasar Iran don yin aikinsu yadda ya kamata, wasu labaran da abin ya shafa kuma wasu kafofin watsa labaru suka bayar ba su da gaskiya.

A ran 25 ga wannan wata a birnin Burushel, babban wakilin kula da harkokin waje da manufofin tsaro na kungiyar tarayyar kasashen Turai Javier Solana ya bayyana cewa, yawan takardun amsa da kasar Iran ta gabatar dangane da shirin kasashe 6 ya kai shafuffuka 20 ko fiye, daga cikinsu, da akwai cikakkun abubuwa da yawa tare da wasu sabon sinadari. A cikin 'yan kwanaki masu zuwa, Mr Solana zai sake yin shawarwari da wakilin farko na yin shawarwari na kasar Iran Ali Larijani ta yadda za a iya tabbatar da fahimfar da za a yi kan amsar Iran yadda ya kamata, kuma za a ba da martani ga amsar kasar Iran kafin karshen watan Augusta.(Halima)