Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-26 18:12:13    
Halin da ake ciki yanzu a kasar Sin game da muhalli ya kai intaha

cri
A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ko da ya ke an sassauta saurin gurbacewar muhalli a kasar Sin a wasu fannoni, amma duk da haka ya zuwa yanzu, halin da ake ciki a kasar game da muhalli ya kai intaha.

Malam Sheng Huaren, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalsiar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi wannan kalami ne ran 26 ga wata a nan birnin Beijing.

An ruwaito cewa, a cikin shekarun nan biyar da suka gabata, kasar Sin ta kashe makudan kudade da yawansu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 840 wajen kyautata muhalli da aka gurbata, ta yi ayyuka masu yawa na shawo kan gurbacewar muhalli da kare yanayin kasa, ta haka an kyautata muhallin birane da garuruwa da yankuna da yawa a wasu fannoni. Amma Malam Sheng Hauren ya bayyana a fili cewa, kasar Sin ta riga ta gamu da matsalolin muhalli wadadan kasashe masu sukuni suka taba samu a cikin kimanin shekaru 100, yayin da suke raya aikin masana'antu na zamani.

Don canja irin wannan hali da ake ciki, yawan kudi da kasar Sin za ta kashe wajen kare muhalli zai kai kudin Sin Yuan biliyan 1400 a cikin shekaru biyar masu zuwa. Kasar Sin za ta gaggauta tace gurbatacen ruwa da ake zubawa cikin manyan koguna da tafkuna na kasar Sin, za ta kyautata iska a birane manya da matsakaita daga duk fannoni, haka zalika za ta yi kokari sosai wajen yin ayyukan gyara juji a birane da garuruwa ba tare da gurbacewar muhalli ba. (Halilu)