|
Ran 26 ga wata da safe, kasar Sin ta yi atisaye mai lambar Tianshan ?1 a birnin Yining na jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, wato atisayen hadin guiwa na zagaye na biyu da ake yi a tsakanin kasashen Sin da Kazakhstan don yaki da ta'addanci.
A lokacin da ake yin wannan atisaye, kasar Sin ta yi amfani da jiragen saman yaki masu saukar ungulu da motocin yaki masu kwantar da tarzoma da sauran makamai. A cikin atisayen da aka shafe sa'o'I biyu da wasu mintoci ana yinsa, sojoji masu yaki da ta'addanci sun yi kazamin fada da 'yan ta'adda, kuma sun hallaka su kwata-kwata. 'Yan kallo sama da 100 wadanda suka fito daga kasar Sin da sauran kasashe na kungiyar hadin kai ta Shanghai suna wurin atisayen. (Halilu)
|