Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-08-26 16:50:04    
Kwamitin musamman na babban taron MDD ya zartas da yarjejeniyar kasa da kasa game da kare hakki da moriyar nakasassu

cri
Ran 25 ga wata da dare, taron da kwamitin musamman na babban taron majalisar dinkin duniya mai kare hakki da moriyar nakasassu ya shirya don kulla yarjejeniyar kasa da kasa game da kare hakki da moriyar nakasassun duk duniya, ya zatars da yarjejeniyar kasa da kasa game da kare hakki da moriyar nakasassu ta hanyar jefa kuri'a.

Makasudin yarjejeniyar nan shi ne domin sa kaimi da kare da kuma ba da tabbaci ga nakasassu wajen more hakkinsu cikin daidaici kuma daga duk fannoni, wadanda suka hada da kiwon lafiya da samun aikin yi da shiga harkokin mulki da rashin nuna musu banbanci da sauransu. An ruwaito cewa, an sa rai za a gabatar da yarjejeniyar nan ga babban taro na 61 na majalisar da za a yi nan gaba ba da dadewa ba don jefa kuri'u a kai. (Halilu)