A kwanakin nan, kasashe uku kamar Faransa da Jamus da Amurka dukanninsu sun nemi kasar Iran da ta daina aikin sarrafa sinadarin Uranium, bisa kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya.
A ran 25 ga wata, Philippe Douste-Balazy, ministan harkokin waje na kasar Faransa ya ce, a cewar, kasar Iran tana son maido da shawarwari a tsakaninta da gamayyar kasa da kasa a kan batun nukiliyar kasar, amma ba ta son daina aikinta na sarrafa sinadarin Uranium, wannan ya saba wa kudurin da kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya zartas dangane da bukace ta da ta daina aikin sarrafa sinadarin Uranium kafin ran 31 ga wannan wata. Daina aikin sarrafa sinadarin Uranium da kasar Sin ta yi, ya zama sharadi ne da ya wajaba ga maido da shawarwarin.
A ran 24 ga wata, Madam Angela Merkel, firayim ministar kasar Jamus ta bayyana cewa, kasar Iran ba ta ce za ta dakatar da aikinta na sarrafa sinadarin Uranimun da maido da shawarwarin ba, yayin da take mayar da martani ga shirin da kasashe 6 suka gabatar game da daidaita batun nukiliyar kasar. Wajibi ne, kasar Iran ta yi karin bayani a kan wannan kalami mai muhimmanci.
Kasar Amurka ita ma ta nanata a ran 24 ga wata cewa, idan kasar Iran ba ta aiwatar da kudurin kwamitin sulhu kafin ran 31 ga wata, to, kasar Amurka za ta dauki matakai wajen kakkabawa kasar Iran ta hanyar kwamitin sulhu. (Halilu)
|