Kwanan baya, ma'aikatar muhalli da slbarkatun kasa ta kasar Kenya ta kafa wata kungiyar aiki, wadda ke tsara matakai wajen yaki da jujin roba.
An labarta a kwanan baya cewa, jujin roba ya kawo wa kasar Kenya matsalolin muhalli da yawa, shi ya sa mutanen kasar suka kara neman gyara jujin roba.
Wannan sabuwar kungiyar aiki za ta tsara sabuwar doka kan gyara juji. Ministan muhalli da albarkatun kasa ta kasar Kenya ya bayyana cewa, kasar Kenya tana yin la'akari da bukatar wasu masu yin amfani da kayayyakin roba da su biya kudi, kamar yadda kasar Afirka ta Kudu ke yi, sa'an nan kuma, ya yi kira ga masana'antun kerar kayayyakin roba da manyan kantuna da su dauki matakai wajen gyara jujin roba.(Tasallah)
|