A ran 25 ga wata, an buga wani labari a shafin labarun kasashen ketare na jaridar "People's Daily" ta kasar Sin cewa, bisa sabuwar kididdigar da gwamnatin jihar musamman ta Macao ta bayar an ce, zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara, karo na farko ne yawan mutane mazaunan Macao ya wuce dubu 500.
Bisa kididdigar da aka yi kuma an ce, yawan mutane mazaunan Macao na yanzu ya kai wajen dubu 503, amma a shekarar 1991 kuwa, yawan mutanenta ya kai fiye da dubu 360 kawai
|